Ramadan: Coci ta raba wa Musulmi da makarantun tsangaya kayan abinci a Kaduna

Faston ya ce shirin na nuna irin haɗin kai da ke tsakanin mabiya addinai a yankin.

Ramadan: Coci ta raba wa Musulmi da makarantun tsangaya kayan abinci a Kaduna

Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Sabon Tasha a Kaduna ta raba wa Musulmi da makarantun Tsangaya da wasu ’yan gudun hijira kayan abinci, albakacin watan azumi.

Babban faston cocin, Yohanna Buru, ya ce an yi rabon ne domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mabiya addinai.

Ya bayyana cewa cocin ta shafe kusan shekaru 20 tana irin wannan tallafi a jihohin Arewa domin taimaka wa marasa galihu su samu sauƙin yin azumi.

Ya ce ban da shinkafa da masara, suna kuma raba tabarma da butocin alwala, tare da kira ga jama’a su yi addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Buru, ya kuma ce sun haɗa fastoci da limamai domin su wayar da kan ’yan kasuwa su rage farashin kayayyaki saboda kamawar Ramadan.

Haka kuma ya yaba da gudunmawar Ramatu Tijjani wajen tallafa wa mabuƙata, yana cewa hakan na nuna kyakkyawar dangantaka tsakanin addinai.

Wasu shugabannin ƙungiyoyi, ciki har da na nakasassu, sun gode wa cocin bisa taimakon, tare da kira ga masu hali su tallafa wa talakawa a watan azumi.

A ƙarshe, wakilan makarantun Tsangaya da malamai sun yaba da shirin, inda suka yi kira ’yan Najeriya su yi koyi da wannan karamci domin ƙarfafa haɗin kai.