Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna

Fasto Yohanna Buru, ya ce sun yi haka ne domin yauƙaƙa dangantaka da kuma wanzar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da makwabtansu mabiya wasu addinai a yankin

Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna

Cocin Christ Evangelical & Life Intercessory Ministry da ke yankin Sabon Tasha a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, ya raba wa makarantun Islamiyya da Musulmi masu ƙaramin ƙarfi akalla 1,000 hatsi albarkacin watan Ramadan.

Shugaban Cocin, Fasto Yohanna Buru, ya ce sun yi haka ne domin yauƙaƙa dangantaka da kuma wanzar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da makwabtansu mabiya wasu addinai a yankin.

Ya ce, “muna mayar da biki ne bisa alherin da Hajiya Ramatu Tijjani, wadda ta tsaya kai da fata wajen rabon shinkafa, kuɗi, da tufafi ga marayu da zawarwan cocinmu a lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara da kuma Ista.”

Fasto Buru, ya ce cocin janyo irin wannan rabon abinci ga Musulmi a jihohi biyar a tsawon shekaru 19, domin sama musu sauƙi a watan Ramadan.

“Bana mun tsara tallafa wa Musulmi 1,000 kuma mun riga mun tanadi buhunan hatsi domin raba musu,” in ji shi.

Ya buƙaci masu hannu da shuni su taimaka wa mabuƙata, tare da roƙon ’yan kasuwa da su guji tsawwala farashin kayan masarufi a watan Ramadan.

Ya ce fastoci da limamai kimanin 30 sun sadaukar da kansu domin gudanar da gangamin kiran ’yan kasuwa su daina ƙara farashin kayan masarufi a watan Ramadan.