Ramadan da Alkur’ani (1)
Daga Hudubar Adil bin Ahmad Bana’imah Masallacin Muhammad Al-Fatih Huduba ta FarkoGodiya da hamdala:Bushara daga gaibi aka jefa ta bakin kogo… a daren ashirin da bakwai ga Ramadan, a lokacin da Annabi (SAW) yake da shekara 40 a duniya, Allah Madaukaki Ya yi izini ga hasken ya sauka. Sai ga Jibrilu (AS) yana matse Annabi […]
Daga Hudubar Adil bin Ahmad Bana’imah Masallacin Muhammad Al-Fatih
Huduba ta Farko
Godiya da hamdala:
Bushara daga gaibi aka jefa ta bakin kogo… a daren ashirin da bakwai ga Ramadan, a lokacin da Annabi (SAW) yake da shekara 40 a duniya, Allah Madaukaki Ya yi izini ga hasken ya sauka. Sai ga Jibrilu (AS) yana matse Annabi (SAW) yana ce masa: “Ka yi karatu! Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ban iya karatu ba. Ya ce, sai ya kama ni ya matse ni har na ji zafi, sannan ya sake ni. Ya ce, “Ka yi karatu.” Na ce: “Ban iya karatu ba.” Sai ya kama ni karo na biyu, ya matse na sake jin zafi, sannan ya sake ni, sannan ya ce “Ka yi karatu.” Na ce: “Ban iya karatu ba. Ya sake kama ni karo na uku, sannan ya sake ni ya ce: “Ka yi karatu da sunan Ubangijinka Wanda Ya yi halitta. Ya halitta mutum daga gudan jini. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka Shi ne Mafi karimci.” (k:96:1-3). Sai Manzon Allah (SAW) ya juya (zuwa Makka) da wadannan (ayoyi) zuciyarsa tana bugawa.” Buhari ya ruwaito.
Haka ayoyin farko na wannan Littafi Mai girma (Alkur’ani) suka sauka a kan Annabi mai tausayi mai jin kai (SAW) a wannan wata mai girma.
Kuma kamar haka ranakunsa masu albarka suka shaidi saduwar sama da kasa, wahayi ya sauka da haske, kasa ta haskaka da hasken Ubangijinta duffan jahilcin Jahiliyya da jahilai suka balbalce.
Kafin hakan, wannan wata mai girma ya shaidi wata saukar wahayin, ita ce saukar Alkur’ani a dunkule daga Lauhul Mahfuz (Tsararren Allo) zuwa Baitul Izza a saman duniya, wannan ya kasance ne a Daren Daraja (Lailatul kadari). “Lallai ne Mu, Mun saukar da shi (Alkur’ani) a cikin Lailatul kadari (daren daraja).” (k:97:1). Kuma: “Lallai ne Mu, Muka saukar da shi (Alkur’ani) a cikin wani dare mai albarka.” (k:44:2).
Ibnu Abbas (RA) ya ce: “An saukar da Alkur’ani a dunkule lokaci guda zuwa saman duniya a daren Lailatul kadari, sannan ya rika sauka bayan haka cikin shekara ashirin.” Nisa’i da Hakim suka ruwaito.
Ibnu Jarir ya ce: “Alkur’ani ya sauka daga Lauhul Mahfuz zuwa saman duniya a Daren Lailatul kadari a cikin watan Ramadan, sannan aka saukar zuwa ga Annabi Muhammad (SAW) bisa abin da Allah Ya yi nufin saukar da shi zuwa gare shi.”
Shi ne daren da aka yi alkawari wanda Allah Ya yi rajistarsa kan ya kasance dukkansa farin ciki ne da jin dadi da annashuwa. Daren hadewar kasa da sama madaukakiya, daren da abu mai girma ya auku wanda bayan kasa bai taba ganin irinsa ba wajen girma da tasirinsa ga rayuwar dan Adam baki daya.
Nassoshin Alkur’ani suna tunatarwa kan wannan babban lamari da ya kunno hasken shiriyarsa daga hasken Mai tausayi, hasken Allah da ke haskakawa daga cikin Alkur’aninSa: “Lallai ne Mu, Mun saukar da shi (Alkur’ani) a cikin Lailatul kadari (daren daraja).” (k:97:1). Da hasken Mala’iku da Ruhi suna masu jijjifi da sauri. “Mala’iku da Ruhi suna sauka a cikinsa.” (k:97:4). Da kuma hasken Alfijir. “Sallama ne shi daren har fitar alfijir.” (k:97:5). (a duba Fi Zilalil kur’an).
Wace ni’ima ce ta fi ni’imar saukar Alkur’ani? Ni’ima ce da godiyar dan Adam ba ta iyar mata, domin Allah Ya gode wa kanSa a bisa wannan ni’ima inda Ya ce: “Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya saukar da Littafi a kan bawanSa, kuma bai sanya karkata ba a gare shi.” (k:18:1). “Wace daukaka ce ga rayuwa da wannan saukarwa yake daukakawa? Lallai ita kyautar Allah ce a kan mutum a bayan kasa. Kyautar da aka haifi mutum tare da ita a matsayin wata sabuwar haihuwa. Mutum ya tashi da ita ya samu sabuwar rayuwa. Kyautar da ta tserar da dan Adam daga wautar Jahiliyya domin ya hau gwadaben da zai jagorance shi zuwa ga daukaka a bisa manhajar Ubangiji Makadaici.” (Fizilalil kur’an).
Don haka ne watan Ramadan ya halarci wannan sauka guda ga Littafin Allah, kuma tun daga wancan rana Alkur’ani ya kulla dangantaka da watan Ramadan. “Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa.” k:2:185). Daga wancan rana watan Ramadan ya zamo watan Alkur’ani.
Za mu cigaba