Ramadan da Alkur’ani (3)

Daga Hudubar Adil bin Ahmad Bana’imah Masallacin Muhammad Al-Fatih Daga cikin alamun kebantar watan Ramadan da Alkur’ani Mai girma akwai Sallar Tarawihi (Asham ko kiyamur Ramadan). Wannan Sallah ce da mafi yawan abin da ke cikinta shi ne karatun Alkur’ani. Kamar dai an shar’anta ta ce domin mutane su saurari Littafin Allah ana kyautata karatunsa, […]

Ramadan da Alkur’ani (3)

Wasu ‘yan uwa Musulmi ne suka yi sujuda a lokacin da suke yin Sallar Tarawihi a Masallacin Qudus (Al-Aqsa) cikin dare.Daga Hudubar Adil bin Ahmad Bana’imah Masallacin Muhammad Al-Fatih

Daga cikin alamun kebantar watan Ramadan da Alkur’ani Mai girma akwai Sallar Tarawihi (Asham ko kiyamur Ramadan). Wannan Sallah ce da mafi yawan abin da ke cikinta shi ne karatun Alkur’ani. Kamar dai an shar’anta ta ce domin mutane su saurari Littafin Allah ana kyautata karatunsa, don haka ne aka so ga liman ya sauke Alkur’ani sauka cikakkiya a cikinta (Tarawihi ko Asham).
Hakika Annabi (SAW) ya kasance yana tsawaita karatun Alkur’ani a cikin Tsaryuwar Ramadan fiye da waninsa. (Lada’iful Ma’arif, shafi na 356). Kuma abin da Imam Ahmad ya ruwaito daga Huzaifa yana karfafa haka. Inda ya ce: “Na zo wurin Annabi (SAW) a wani dare na Ramadan, sai ya tashi zai yi Sallah. Lokacin da ya yi kabbara ya ce: “Allahu Akbar zul malakuti wajjabaruti walkibriya’i wal azamati, sannan ya karanta Bakara sannan Nisa’i, sannan Ali Imrana, bai wuce ayar da take da tsoratarwa face ya tsaya a wurinta. Sannan ya yi ruku’u yana mai ce: “Subhana rabbiyal azimi,” misalin yadda ya kasance a tsaye, sannan ya daga kansa, ya ce, “Sami’allahu li man hamidahu, Rabbana lakal hamd,” misalin abin da yake tsaye, sannan ya yi sujada, yana cewa: “Subhana rabbiyal a’ala,” misalin yadda ya kasance a tsaye, sannan ya dago kansa ya ce: “Rabbi gifirli,” misalin yadda ya ksance a tsaye, sannan ya dago kansa ya mike. Bai sallaci komai ba face raka’a biyu, har Bilal ya zo ya yi kiran Sallah.” (Ahmad, Musnad baki Musnadil Ansar, lamba na 22309).
Kuma hakika Umar (RA) ya umarci Ubayyu bin Ka’ab da Tamimud Dari su rika yi wa mutane limancin Sallar Asham a watan Ramadan, wani mai karatun yakan karanta aya 200 a raka’a daya har ya kai mutane suna dogara da sanda saboda dogon tsayuwa, ba su  idarwa sai daf da alfijir. A wata ruwayar kuma suna daure duwatsu a tsakanin katanga sannan su jingina a jikinsu. ( Lada’iful Ma’arif shafi na 356).
Wasu daga cikin magabata sun kasance suna sauke Alkur’ani a Sallar Asham a kowane dare uku na Ramadan, wasu a kowane dare bakwai daga cikinsu akwai kattada. Wasu kuma a kowane dare goma daga cikinsu akwai Abu Rija’u Al-Addaridiy. (Lada’iful Ma’arif, shafi na 358). Duk wannan tsaiwatawa da tsayuwar dare domin a yi tilawar Alkur’ani ne a haskaka dararen Watan Alkur’ani su rika haske da ayoyin Alkur’ani.
Idan wannan shi ne sha’anin Alkur’ani a cikin Ramadan, me bawa yake jira ba zai rungume shi ba, ya dauwama wajen nazari a cikinsa. Ina ba dan uwa mumini na gaskiya shawarar ya kasa lokacinsa gida uku don ganawa da Alkur’ani a wannan wata.
Lokaci na farko: Hira wajen yawaita tilawa da maimaita saukarsa. Sai mutum ya sanya wa kansa wani jadawali da zai rika kiyayewa ta yadda zai iya sauke Alkur’ani da yawa domin ya samu alherori ya ni’imtu da albarka mai yawa.
Lokaci na biyu: Lokacin bata dare yana nazari da tadabburi. Sai mutum ya samu budi a cikin wannan wata ta akalla ya dauki shafi daya ko makamancinsa yana muraja’ar tafsiri da nazarin ma’anarsa da kokarin gano dalilai da fitar da umarce-umarcen da hane-hanen da ke ciki, sai kuma himma domin dabbaka hakan a rayuwarsa da yi wa kansa hisabi a kai. Babu laifi mutum ya tsawaita lokacin sauke wannan fasali na karatu zuwa shekara daya ko fiye. Mai karatu ya yi tsari kuma ya yawaita nazari tare da yin aiki da kansa a cikinta, kila hakan yana daga cikin ma’anar maganar Sahabi mai girma cewa: “Mun kasance muna koyon ayoyi goma ba mu wuce su har sai mun san abin da ke cikinsu na ilimi da aiki.”     
Kashi na uku: Lokacin hadda da muraja’a. Sai mutum ya tsara wa kansa misali yinin daya na haddace wani abu da yin muraja’a. Idan kuma ya haddace wani abu amma ya manta, to dama ce babba ya tabbatar da haddar ya dawo da abin da ya kubce masa. Ba sai na yi bayanin martaba da matsayin mahaddata Littafin Allah ba, ya ishe shi cewa yana daf da Annabta sai dai ba a yi masa wahayi.  
dan uwa mai girma! Ka san wani abu daga falalar Alkur’ani gwargwado, kuma ka san yadda wannan wata mai girma yake harde da Alkur’ani Mai girma gwargwado, don haka babu abin da ya saura face ka zage dantse, ka yi azama ka cije ka kasance tare da Alkur’ani.
“Ya bayin Allah! Wannan shi ne watan Ramadan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, a cikinsa akwai abin jin dadi ga masu ibada. Wannan shi ne Littafin Allah da ake karanta shi a tsakaninku kuma ake jin sa. Shi ne Alkur’ani wanda da a ce an saukar da shi a kan dutse ne da ka gan shi yana mai kankan da kai yana farfashewa. Amma a tare da haka babu zuciyar da take jin tsoro! Kuma babu idanun da yake zubar da hawaye! Kuma ba azumin da yake kangewa daga aikata haram balle ya yi amfani? Kuma tba sayuwar Ramadan da ta daidaita, balle ma’abucinta ya yi fatar samun ceto!” (Lada’iful Ma’arif, shafi na 364-365).
To shin rai zai juyo? Ko kuma shin zuciya za ta ji tsoro? Shin za mu cika watan Alkur’ani da tilawar Alkur’anin?