Ramadan: Gidauniyar Dangote ta raba buhunan shinkafa miliyan ɗaya a bana

Baya ga rabon burodi da ake yi a shekara 4, an shafe sama da shekara 30 ana ci gaba da ciyar da mabuƙata a Kano

Ramadan: Gidauniyar Dangote ta raba buhunan shinkafa miliyan ɗaya a bana

Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun Gidauniyar Aliko Dangote, ya ƙaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmi su dubu 10 a Jihar Kano, jiharsa ta asali.

Har ila yau gidauniyar ta kara yawan abincin da take ciyarwa ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan ɗaya da kuɗinsa ya haura Naira biliyan 13 a jihohi 36 da Abuja domin rage halin matsin yunwa da al’umma ke fama da shi a kasar nan.

Manufar wannan aiki shi ne a saukaka wa miliyoyin ’yan Nijeriya wahalhalun da suke ciki da kuma ƙalubalen tattalin arziki da ake fama da shi.

Baya ga raba burodi dubu 20 da ake yi kullum ga mazauna birnin Kano da dubu 15 ga mazauna Legas, wannan ciyarwa ta abincin da aka fara tun lokacin cutar Kwarona a 2020 ta dore har zuwa yanzu.

Abincin da ake dafawa ana rabawa sun haɗa da shinkafa dafa-duka, shinkafa da miya, dafa dukan taliya, doya, wake da naman kaji da na shanu da robar ruwa ga kowane mutum ɗaya.

Ana raba ƙunshin abincin ne a masallatan Juma’a da tituna da gidajen yari da gidajen marayu da sauran wurare a birnin Kano da kewaye.

Wani wanda ya ci gajiyar abincin mai suna Malam Musa Maikatako mazaunin Unguwar Tarauni ya bayyana jin daɗinsa da wannan karamci, ya ce ya taimaka masa wajen yin buɗa-baki cikin sauƙi.

Malam Maikatako, ya ce samun wannan abinci na kyauta zai taimaka wajen rage wa al’umma wahalhalun da suke ciki, wanda in ba don wannan abinci ba, jama’a da dama ba za su iya yin buɗa-baki sai da ruwa kawai, ganin matsalar tattalin arziki da ’yan Nijeriya ke fuskanta.

“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, wannan abinci ya taimaka matuƙa ga talaka irina, domin mun samu abin da za mu yi buɗa-baki baki da abinci mai kyau.

“Na san mutane da yawa a jihar nan waɗanda za su yi buɗa-baki da ruwa kawai. Don haka wannan abinci ya kawo mana sauƙi,” in ji shi.

Malam Musa Maikatako ya yi godiya ga Gidauniyar Dangote bisa wannan karimci, inda ya yi addu’ar Allah Ya ƙara masa arziki ya kuma ci gaba da sanya albarka a kasuwancinsa.

Wata wadda ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin daɗinta ga rabon abincin, wanda a cewarta Gidauniyar Aliko Dangote ta kawo mata ɗauki.

A cewar Inna, “Na yi farin ciki da na samu abinci mai daɗi kuma kyauta a cikin irin wannan hali na wahalhalu da ake ciki. A cikin wannan wahala da muke ciki a ce ka samu abinci irin wannan ai sai godiya.

“Ba abin da zan ce sai dai in yi godiya ga Alhaji Aliko Dangote, ina roƙon Allah Ya ƙara masa albarka,” in ji Inna.

Baya ga rabon burodi da ake yi a shekara 4, an shafe sama da shekara 30 ana ci gaba da ciyar da mabuƙata a Kano da Gidauniyar Aliko Dangote ke yi.

Ana yin haka ne daga gidan mahaifiyarsa da ke Koki da wuraren girki daban-daban da aka tanada.

Wannan shirin ciyarwa yana ciyar da mazauna Kano dubu 10 a kullum tare da samar da abin karin kumallo da abincin rana da kuma abincin dare, duk wannan aiki mai tarin fa’ida ana gudanar da shi fiye da shekara 30.