Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki

Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan.

Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki

Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan.

Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma  gudanar da ibada a wannan wata mai albarka.

Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya koma karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Litinin zuwa Alhamis.

Sanarawar ta kara da cewa ranar Juma’a kuma za a rika tashi aiki karfe 1 na rana har zuwa karshen watan azumin.

Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su yi amfani da watan ibadar wajen yin addu’o’in samun sauki a fannin tattalin arziki da zaman lafiya a Jihar Jigawa da ma kasa ba ki daya.