Ramadan: Hanyar magance sabanin ganin wata —Farfesa Mansur
Ya bayyana yadda za a mangace matsalar da ke kawo sabanin ganin wata a Najeriya
Malamin addini Musulunci a Najeriya, Sheikh Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto, ya ce hanyar magance sabanin ganin watan azumi shi ne kawai a ba wa Sarkin Musulmi ikon tilastawa a bi umarni.
- Matashi ya fille kan kakarsa ya kai ofishin ’yan sanda
- Dalilai uku na sauke Sufeto Janar Mohammed Adamu
- ‘Tun ina shekara bakwai mahaifina yake kwanciya da ni’
A duk shekara akan samun sabanin ganin watan Azumin Ramadan a Najeriya, yaya kake kallon kokarin da Sarkin Musulmi yake yi na ganin an kauce wa sabanin ganin wata a cikin al’umma?
Duk kasashen dana sani na Larabawa —Suddan, Masar, Saudiyya Tunisiya, Moroko, Kuwait, Katar da sauransu— hukuma ce take bayar da sanarwar ganin wata, babu wanda ya isa ya yi jayayya.
Shi ne ya sanya ba ka samun jayayya a can sai a wurinmu, domin a nan karfin Sarkin Musulmi na zartarwa yana hannun gwamnati, don haka ba za a daina sabani ba har abada.
Amma idan ana karantar da mutane rikici yana raguwa, kasan hakkinka ne ka duba wata, mai tabbatarwa —Sarkin Musulmi— kuma a bar shi ya yi nashi aiki. Amana ce hannun sarkin Musulmi.
Mece ce maslahar Sarkin Musulmi idan ya sanya muka yi azumi ba daidai ba miye fa’idarsa a ciki?
Kwamitoci ake da su a kasa da majalisa da kananan hukumomi da ke tabbatar da ganin wata, Sarkin Musulmi fada ne kawai nasa.
Addinin Musulunci bai taba wulakanta ilimi ba, yanzu zamani ya zo da ake da ilmi da yake iya fadin lokacin da za a haifi wata da lokacin da za a iya ganin sa da injin da kuma lokacin za a iya ganinsa da idanu.
Idan ilimi ya tabbatar da ana iya ganin sa wani ya zo ya ce ya gani za a iya sauraren sa.
Amma idan ilmi ya tabbatar da abin nan ba a ma haife shi ba, misali, za a iya haihuwar sa tara na dare, kai kuma ka ce ka gan shi 7:10, ka ga ke nan maganarka ba ta da muhalli.
Idan Sarkin Musulmi ya ce bai aminta da ganinka ba, bai kamata ka tilasta a karbi abin da ba gaskiya ba ne.
Saboda amana ta yi karanci a cikin mutane, akwai masarautar da aka kawo labarin ganin wata da hatimin sarkin a kan takardar bayanin mutanen da suka ga wata.
Da aka tafi garin babu mutanen su 10, sakataren da ya rubuta takardar ya gudu saboda takardar karya ya rubuta sarkin bai sani ba.
Ana haka sai Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya ce ya gani a yarda?
Kwamitin ganin wata na kasa yana tare da manyan malamai masu ilmin taurari da shari’a, su ne suke yanke shawarar kan ganin wata; ba su yi don son zuciyarsu, suna yi ne don maslahar al’umma a yi ibada yadda ya kamata.
In ka ce duk mai jama’a ya ba su umarni kan ganin wata al’umma ba za ta yi azumi tare ba.
Annabi (SAW) ya ce azumi tare ake yi da jama’a haka ajiyewa da sallar layya, abu ne da ake son a yi tare, a kan haka ake da jagora na koli da ake bi wanda shi ne cibiya da ake bi.
Matsalarmu a nan, duniya sun yarda da shugabanninsu amma mu ba haka ba.
Allah shi ne shaida, shugabannin Larabawa mun san raunin addininsu mun san namu sun fi da yawansu, amma can sun amince da su, suna yi musu biyayya don suna da karfin zartarwa, don in ka saba ana iya hukunta ka, amma mu akwai wannan gibin, mu dai al’ummar Musulmi mu rika duba duk wani abu da za mu aikata a yi yadda shari’a ta ce.
Malam a watan Azumi talauci ne ya yi wa kasar nan yawa ko karancin masu kudi ake da su domin ciyarwa da ake yi a watan Ramadan ba ta wadatar ga wadan da ake bai wa ba?
Su dai malamai a kowane watan azumi suna kira sosai a taimaka wa bayin Allah, matsalar ita ce al’ummarmu ta yanzu taimako ya yi karanci cikinta, zuciyar rahama da tausayi ta yi karanta a cikin mutane, duk da bai kamata mu rufe ido ga abin da ke gudana na alheri da yawan attajirai ba. wasu na taimakawa har gwamnati tana yi, bai kamata mu raina kadan da ake yi ba, babu laifi kuma hakan albarkacin karantarwa ne da ake yi.