Ramadan: Hisbah ta kama marasa Azumi 12 a Kano

Waɗansu daga cikin matasan sun ce ba su da labarin ganin wata saboda ba su da wayar salula ballantana rediyo.

Ramadan: Hisbah ta kama marasa Azumi 12 a Kano

Jami’an Hisbah

Dakarun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta samu nasarar kama wasu matasa 12 da ake zargin ba sa yin Azumi a wannan wata na Ramadana.

Hukumar Hisbar ta cafko matasan ne a wani samame da ta kai a wuraren da suka haɗa da, yankin Asibitin Murtala, Titin Kofar Wambai, France Road, Igbo road, Kasuwar Bata, ’Yankaba da kuma Kasuwar Mallam Kato.

Ana zarginsu da yin kunnen kashi bayan an sanar da ganin sabon jinjirin watan Azumin Ramadan amma suka yin azumin a ranar farko.

Sai dai matasan sun bayyana cewar su a gidansu sai sun ga watan da idanunsu biyu sannan suke ɗaukar Azumin, sannan ba su san cewar an ga watan ba sakamakon ba su da wayar salula ko rediyo.

Wasu daga cikin ababen zargin sun haɗa da Danjuma Ibrahim mai shekaru 20 dan asalin Jihar Katsina da aka samu yana cin Rogo a cikin Kasuwa.

Haka kuma, an kama wani mai suna Abdullahi Sulaiman mai shekaru 33, mazaunin Gezawa, wanda ya bayyana cewar ya tashi da niyyar yin Azumin amma ciwon Olsa ne yake damunsa shi ya sa bai ɗauka ba.

Haka zalika, akwai wani mai suna Lawan Ado Katsina, inda ya bayyana wa jami’an Hisbar cewar ya ci Rogo da ruwa a Kasuwar Sabon Gari.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbah, Dokta Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya bayyana cewar ba za su ɗaga wa Gandayen ƙafa ba, domin za su ci gaba da gudanar da samame a lungu da saƙo na faɗin Jihar Kano.

Hukumar ta Hisbah dai ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen shiga dukkan lungu da saƙo a jihar domin kama gandaye.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos