Ramadan Kareem: Kira ga ’yan uwa Musulmi
Assalam. Ina taya daukacin al’ummar Musulmi barka da zagayowar watan Ramadan mai Albarka. Shawara ga yan’uwa musulmi, mu dukufa wajen taimaka wa junanmu, ta hanyar yawaita kyauta da sadaka a cikin wannan watan mai alfarma. Mu sani akwai dubannan mutane da ba sa samun abincin da za su yi sahur ko buda baki bayan an […]
Assalam. Ina taya daukacin al’ummar Musulmi barka da zagayowar watan Ramadan mai Albarka. Shawara ga yan’uwa musulmi, mu dukufa wajen taimaka wa junanmu, ta hanyar yawaita kyauta da sadaka a cikin wannan watan mai alfarma. Mu sani akwai dubannan mutane da ba sa samun abincin da za su yi sahur ko buda baki bayan an sha ruwa. Da yawa daga cikin irin wadannan mutanen ba sa iya fadin halin da suke ciki ga kowa ballantana su nemi taimako don a taimaka musu. Wasun su kan nemi taimako a wajen ‘yan uwa da abokan arziki don samun damar gudanar da ibada a cikin sauki. Yakamata kowa ya duba a cikin unguwar su, ko kasuwa, ko wajen aiki, ko masallacin da yake zuwa yin sallah. Duk wanda yake da bukatar taimako ya taimaka masa muddin yana da halin taimakawar. Yin hakan zai kara kulla zumunci da soyayyar juna a tsakaninmu. Da taimakawa ‘yan uwa za a samu saukin gudanar da ibada a cikin wannan wata mai alfarma. Daga Mansoor S. PRP Kano 07039215954 .