Ramadan: Matashiya ga mata
Azumi na daya daga cikin shika-shikan musulunci, babu wanda ya san ladan da ke cikinsa, kasancewar Allah (SWT) Ya ce azumi nasa ne, kuma Shi kadai Ya san irin ladan da yake ba duk wanda ya yi azumi don Shi. A sakamakon haka ne ya sanya zan yi wa mata wata matashiya da ke kunshe […]
Azumi na daya daga cikin shika-shikan musulunci, babu wanda ya san ladan da ke cikinsa, kasancewar Allah (SWT) Ya ce azumi nasa ne, kuma Shi kadai Ya san irin ladan da yake ba duk wanda ya yi azumi don Shi. A sakamakon haka ne ya sanya zan yi wa mata wata matashiya da ke kunshe da ayyukan da ya kamata su rika yi a cikin watan azumi, don kara samun falala da kuma lada, kasancewar akwai wadanda za su yi azumi amma a karshe ba za su tsira da lada daidai da kwayar zarra ba, ma’ana sun yi kishin ruwan banza.
A yawan lokuta mata kan bata lokacinsu wurin kallace-kallacen fina-finai ko sauraren wakoki, a cewarsu hakan na cinye musu lokaci, har su kai azumi ba tare da sun sha wahala ba, sai dai abin da ba su sani ba shi ne, hakan ba zai haifar wa azuminsu da mai ido ba. Wasu kuma sukan taru su rika hirarraki marasa ma’ana, ko su rika maganganu marasa kan gado da a karshe maimakon su samu ladan azumi, sai kuma su samu zunibi.
Idan har lokaci kuke so ku cinye yayin azumi, a lokaci guda ku samu lada mai dimbin yawa, to sai ku rika aikata abubuwan da zan yi muku bayaninsu a cikin wannan matashiyar.
Sallolin farilla da kuma ta nafila
Yana da kyau ku rika sallolin farilla a kan lokaci, ku sani idan sallah ta yi kyau to sauran ayyuka ma za su yi kyau, don haka idan kuna so azuminku ya samu tagomashi sai ku rika sallolin farilla a kan lokaci.
Ya kamata ku rika yin sallolin nafila kasancewar suna cika sikilen bawa. Kada ku ce kun yi aikin gida don haka kun gaji, a’a, ku daure don yin sallolin nafila. Ku tashi cikin dare musamman salusin karshe.
Karantawa da sauraren karatun al-kur’ani:
Ku dage wajen karantawa hade da sauraren karatun kur’ani, kasancewar karantawa da kuma sauraren karatun kur’ani turare ne ga ruhi, sukan kwantar da hankalin zuciya, kuma abinci ne ga ruhi.
Abu Nu’aim ya yi bayani a cikin Tib an-Nabbi cewa manzon Allah (SAW) ya ce, akan samu karuwa mai yawa a lokacin da mai sauraron karatun kur’ani ya fahimci ma’anar karatun. Allah (SWT) Ya ce “Kuma wadanda suka nisanci shadainu ga bauta musu, kuma suka mai da al’mari ga Allah, suna da bushara. To ka bayar da bushara ga bayiNa. Wadanda ke sauraren magana, sa’annan su bi mafi kyawunta. Wadancan su ne Allah Ya shiryar da su, kuma wadancan su ne masu hankali. (Sura ta 39 aya- ta 17 zuwa 18).
Bayin Allah na kwarai su ne wadanda suke sauraren kur’ani kuma suke dagewa wurin yin aiki da shi. Don haka idan kuna karanta kur’ani ko kuma sauraren karatun kur’ani za ku samu dimbin lada, kuma za su cinye muku lokacin da kuke so maimakon ku rika kallace-kallace ko sauraren kade-kade da wake-wake.
Yin Zikiri
Ku kasance masu yin zikiri domin zikiri ma zai taimaka wurin cinye lokaci, kuma zai sanya ku samu dimbin lada da kuma gafarar zunubi daga Ubangiji (SWT).
Mu’azu Ibn Jabal ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce: “Yan aljanna ba za su taba da-na-sani ba sai a kan abu guda, wato za su yi da-na-sanin ne idan suka tuna wata sa’i da za ta wuce ba tare da sun tuna ko sun ambaci Allah ba.” Bayhaki ne ya rawaito a cikin Shu’abal-iman (1:392 shafi na 512 zuwa 513)
Saboda haka ya kamata ku rika tuna Ubangiji ba wai sai a lokacin azumi ba.
Ba dole sai kun ware wani lokaci ko kuma kun kadaice, ko kun rufe kanku a daki kafin ku yi zikiri ba, a’a, za ku iya hakan ko a lokacin da kuke girki-girke, ko sharar tsakar gida ko daki ko falo, za ku iya zikiri a lokacin da kuke gyara gado, ko wanki da wanke-wanke da sauransu, abin da ake bukata shi ne ku rika yi a zuciyarku, ko kuma a hankali. Abin da ba a so shi ne ku rika daga murya da karfi.
Ga misalan zikirin da za ku rika yi ko da ba a lokacin watan azumi ba:
1 Allahumma innaka ‘afuwwun tuhibbul ‘afwa fa’fu ‘annee
2. Subhaanallah 3 Alhamdulillah 4 Allahu Akbar 5 Laa ilaaha illallah 6 La hawla wa la kuwwata illa billah-hil aliyyil adheem 7. Asthaghfirullah halladhee Laa ilaaha illa huwal Hayyul kayyuumu Wa’athuubu Ilai 8 Sub haanallaahi wa bi hamdihi sub haanallahil adheem 9 Subhanallahi, wal-hamdu lillahi, wa la ilaha illallahu, wal lahu akbar. Wa la hawla wa la kuwwata illa billahil aliyyil azim. 10 La ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, yuhyi wa yumuttu wa huwa hayyu illa yumutu abadan abada, dul jalali wal ikram, biyadihil khayr, wa huwa ala kulli shay in kadir. 11 Laa ilaaha illal laahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa huwa alaa kulli shay’in kadir.
Za mu ci gaba