Ramadan: Matashiya ga mata (2)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba rubutun da muka fara kawo muku:Addu’aYa kamata ku rika gudanar da addu’o’i hade yin nadama kan ayyukan sabo da kuka aikata. Za ku yi hakan ne da safe da rana da yamma da kuma da daddare- ma’ana a kowane lokaci. Kada ku bari […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba rubutun da muka fara kawo muku:
Addu’a
Ya kamata ku rika gudanar da addu’o’i hade yin nadama kan ayyukan sabo da kuka aikata. Za ku yi hakan ne da safe da rana da yamma da kuma da daddare- ma’ana a kowane lokaci. Kada ku bari kasala da lalaci ko kuma ku ce gajiyar aiki ta hana ku.
Ku ambaci Ubangiji zai saurare ku, domin Allah (SWT) Ya fada wa Manzon Allah (SAW): “Kuma idan bayina suka tambaye ka daga gare Ni, to lalle Ni makusanci ne. Ina karbar kiran mai kira idan ya kira Ni, saboda haka su nemi karbawaTa, kuma su yi imani da Ni: tsammaninsu su shiryu.” al-kur’ani 2, Aya ta 186).
Manzon Allah (SAW) Ya ce: “Babu abin da yake da kima da daraja a wurin Allah fiye da addu’a daga wurin bayinsa.” (Sahih al-Jami hadisi na 5268).
Don haka ku roki Allah Ya yafe muku laifuffukan da kuka aikata, domin Allah Yana son masu tuba. Lokutan da Allah Ya fi amsa addu’a sun hada da:
1. Sulusin karshe na dare 2 Lokacin da bawa ke azumi 3 Tsakanin sallar la’asar da kuma maghrib 4 Dakiku kadan kafin a fara azumi 5 A ranar Juma’a kafin da kuma bayan huduba 6. Tsakanin kiran sallah da kuma ta da ikama 7. Lokacin da ake ruwa 8 Bayan an karanta kur’ani 9 Daren Lailatul kadr.
Don haka kada ku yarda azumi ya wuce ba tare da kun yi ayyuka da kuma addu’o’in da Allah Zai gafarta muku ba. Domin Manzon Allah (SAW) ya ce, wata rana mala’ika Jibril ya zo wurinsa sai ya ce Allah Ya tsine wa duk wanda watan Ramadana ya zo har ya wuce ba tare da ya aikata ayyukan da Allah Zai gafarta masa ba, inda kuma Manzon Allah ya ce Amin. (al-Bukhari da al-Tabrani suka rawaito shi).
Don haka ku roki Allah Ya karbi kyawawan ayyukanku, ya kuma gafarta muku zunubanku. A lokacin da kuke addu’a ana so ku sanya yakinin Allah Zai karbi addu’arku.
dabi’u da halaye nagari
A lokacin da kuke azumi bai kamata ku rika nuna wadansu halayen ko dabi’un da ba su dace ba, ma’ana ku rika yin maganganun da ba su dace ba, hakan ya sanya Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafiya fifikon alheri a cikinku su ne wadanda suke da halaye da dabi’u na kwarai. (al-Bukhari)
Ya kuma ce: “Babban abin da yake cika sikeli a ranar sakamako shi ne dabi’a ta kwarai ko hali nagari (al-Tirmidhi da Abu Dawud suka rawaito shi).
Ku dubi falalar da ke cikin nuna halaye da dabi’u nagari? Don haka nake fata za ku kasance masu nuna halaye da dabi’u nagari.
Kada ku manta Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wadanda na fi so kuma suke kusa da ni a ranar alkiyama su ne wadanda suke da halaye da dabi’u nagari. Wadanda na tsane su kuma suke nesa da ni su ne wadanda suka fiye yawan magana da kuma dagawa ko jiji da kai. (Tirmidhi ne ya rawaito shi)
Saboda haka ba sai a watan azumi ya kamata ku rika nuna halaye da dabi’u masu kyau ba.
Sadaka
Ya kamata ku yawaita sadaka a lokacin watan Ramadana da kuma bayansa, domin sadaka takan cinye munanan ayyukan kamar yadda wuta take cinye auduga.
Am fi so idan za ku sadakar to ku yi ta a boye, domin Manzon Allah ya ce: “Kyawawan ayyuka na kare dan Adam daga yin mummunan karshe, kuma sadakar da aka yi ta boye takan kawar da fushin Allah (SWT)….” Al-Tabarani ne ya rawaito shi)
Kawar da duk wani abu da zai cutar da jama’a daga kan hanya sadaka ce. Idan magidanci ya kawo abin da iyalinsa za su ci sadaka ne, haka ko mata za ta dafa abincin don iyalinta sadaka ce da sauransu.
Allah Ya sa muna daga cikin wadanda za a yi wa rahama da gafara da kuma samun ’yanci, amin.