Ramadan: Sarkin Saudiyya zai ba ’yan Najeriya 12,600 abinci

Iyalai Musulmi 2,300 a Najeirya ne za su amfana da kayan abinci a watan Ramadan

Ramadan: Sarkin Saudiyya zai ba ’yan Najeriya 12,600 abinci

Sarki Salman Bin Abdulazeez na Saudiyya

Gidauniyar Sarki Salman na kasar Saudiyya (KSrelief) za ta ciyar da ’yan Najeriya 12,600 ta hanyar raba wa iyalansu kanyan abinci a watan Ramadan da ke kara karatowa.

Gidauniyar ta bayyana cewa iyalai Musulmi 2,300 a Najeriya ne za su amfana da tallafin kayan abincin a watan Ramadan, domin su samu saukin rayuwa.

Ta bayyana haka ne a lokacin da take kulla yarjejeniya bayar da aikin ciyarwar da kungiyar jinkai ta Abibakr As-Sidiq Philanthropic Home (ASPH), wadda ta ba wa aikin rabon kayan abincin ga iyalan da za su amfana da tallafin.

Da suke sanya hannu a kan yarjejeniyar a Abuja, KSrelief da ASPH sun bayyana cewa manufar aikin ita ce ciyar da ’yan Najeriya Musulmi 12,600 da ke fama da matsanancin talauci.

Wadanda suka sanya hannu a yarjejeniyar ciyarawar su ne Wakilin KSrelief, AbdulKarim bin Abdulmohsen Al-Yousef tare da Mataimakin Shugaba Mai Kula da Ayyuka na Musammana a ASPH, Sultan Mohammed Saleh, wanda ya wakilci shugaban ASPH, Abdulrazzaq Ibrahim Salman.