Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250

Ya jaddada cewar Saudiyya za ta ci gaba da tallafa wa waɗanda ba su da ƙarfi.

Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250

Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Jihar Kano, ya bai wa jihar da wasu jihohin Arewa kyautar dabino katan 1,250, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin Ramadan na kowace shekara.

Wannan shiri na cikin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarki Salman (KSrelief), ke gudanarwa don tallafa wa masu buƙata da kuma ƙarfafa dangantakar Saudiyya da Najeriya.

Yayin bikin rabon dabinon, Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Admawy, ya gode wa Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa ƙoƙarinsu na ci gaba da tallafa wa al’ummar Musulmi a faɗin duniya.

Ya jaddada aniyar Saudiyya na ci gaba da taimaka wa Musulmai, musamman a lokacin watan Ramadan.

A bana, Saudiyya ta ware tan 50 na dabino don raba wa a Kano da wasu jihohin Arewa, baya ga tan 60 da aka riga aka aike Abuja a makon da ya gabata.

Ana ci gaba da shirin rabawa don tabbatar da cewa dukkanin kayan sun isa hannun buƙata.

Jakadan Saudiyya, ya kuma bayyana cewa shirin buɗa baki na ƙasar zai fara aiki ne a Abuja a ranar 3 ga watan Ramadan, inda za a raba wa Musulmai masu azumi abinci kyauta.

Ya kuma yi bayani kan irin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarkin ke yi a duniya, inda ya ce tuni cibiyar ta kammala sama da ayyuka 2,500 da darajarsu ta haura dala biliyan bakwai, waɗanda suka amfanar da ƙasashe 91.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Farouk, ya wakilta, ya nuna godiyarsa ga wannan kyauta.

Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta tabbatar da cewa an raba dabinon ga waɗanda suka dace su amfana.