Ramadan: Saudiyya ta fara rajistar masu ciyar da abincin bude baki

Masu son ba da sadakar abincin bude-baki a Masallacin Harami za su fara rajista

Ramadan: Saudiyya ta fara rajistar masu ciyar da abincin bude baki

Daga: www.rtvonline.com

Kasar Saudiyya ta fara rajistar masu ciyar da abincin bude-baki sadaka a watan Azumin Ramadana mai kamawa a Birnin Makkah.

Gwamnatin Saudiyya ta ce masu neman izinin ba dasadakar abincin bude-baki a Masallacin Haramin Makkah da harabarsa da suran unguwannin birnin na da damar yin rajistar neman gurbi.

Ta kuma fara bayar da lasisi ga kamfanonin da za su yi aikin tantancewa da kayyade yawan mutanen da za a ciyar da tsarin rabon abincin bude-bakin.

“Hukumomin da ke alhaki ne za su yi alkalanci wurin bayar da lasisin bayan kayyade adadin mutanen da za a ciyar da kuma tsarin rabon  abincin,” inji sanarwar.

Ta ce masu sha’awar samun izinin na iya ziyartar shafin hukumar na intanet domin neman gurbi.

Karon farko ke nan za a ci gaba da ciyar da masu azumi bayan tsaikon da aka samu sakamakon bullar cutar COVID-19 wadda takuma tilasta takaita yawan masu shiga masallatan harami da mahajjata a 2020.

Bullar cutar ta sa Saudiyya dakatar da ciyar da abincin bude-baki sadaka a Masallatan Haramin Makkah da Madinah a watan Ramadan da ranakun azumin nafila a matsayin matakin hana yaduwar cutar.