Ramadan: Tanadi ga maigida

Dadin abinci kadai bai samar da soyayyar namiji sai an hada da kulawa.

Ramadan: Tanadi ga maigida

Ma’aurata

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Tambaya: Zuwa ga Duniyar Ma’aurata, Ina son a ba ni shawarar hanyoyin da zan bi wajen kayatar da maigidana a cikin wannan wata na azumi.

Domin ina da matsalar in ina shayarwa sai in ji ina kyamar kusantar ibadar aure.

To maigidana ya lura da haka sai yake dan saukaka min bai cika matsa min a kan haka ba.

To ga shi yanzu na yaye yaron da nake goyo kuma maigidana ya yi wajen wata shida ba ya gida amma zai dawo gab da azumi, shi ne na ce bari in nemi shawararki kan hanyoyin da zan faranta wa maigida a cikin wannan wata mai albarka na Ramadan. -Mai son mijinta

Amsa: Hakan ya yi kyau da kike son kyautata wa mijinki sakamakon kyautatawarsa gare ki.

Kamar yadda Ayar Alkur’ani ta tabbatar cewa babu wani sakamako da ya dace da kyautatawa face kyautatawa.

Don nuna godiya ga kyautatawar mijinki gare ki sai ki bi wadannan hanyoyin:

Ki nuna masa godiyarki ta halaye wato sai ki bincika cikin halaye da dabi’unki, in akwai wanda maigidanki ya nuna ba ya so, ko wanda yake yawan korafi ki daina, ki rika kokari, ki horar da kanki da zuciyarki wajen ganin kin goge wannan hali daga dabi’arki.

In kuma na yi ne sai ki dage ki fara aikatawa kuma ki nace har sai hakan ya zamar miki dabi’a.

Misali, maigida yana yawan yi miki korafin bai son zagi, ko bai son zama da daurin gaba, ko bai son a bar kwanukan abinci su kwana ba a wanke ba, ko ya ce bai son kina hulda da maza a kafofin sadarwar zamani, ko wani abu makamamcin haka.

To don nuna godiyarki ga kulawarsa sai ki gyara, musamman in abu ya shafi hakkinsa na auratayya.

Binciken masana kimiyyar halayyar dan Adam ya tabbatar da cewa duk wani hali ko dabi’a da ake son ta kafu cikin ma’aikatar hankali, to, in dai aka rika aikata wannan hali ko dabi’a na tsawon kwana ashiri da daya to shi ke nan ta kafu a cikin ma’aikatar hankali a matsayin hali ko dabi’ar wanda ya aikata su.

Ki gyara gidanki don armashin maigidanki: Abin nufi ki yi gyara da tsara gidanki daidai da yadda zai nishadantar da maigidanki.

Yawanci ana yi kwalliya a dakunan gida da yanayin kwalliya irin na ’ya mace.

To kamar yadda akwai ’yanci wajen yanayi da launin kayan sawar mace da na namiji, to haka ma akwai banbancin kwalliya da irin tsarin da ake yi wa dakuna kwana da na hutawa.

Mace tana son jera abubuwan kwalliya iri daban-daban, mace tana son launuka masu walkiya, masu cizawa da kuma daukar ido, yayin da namiji ba ya son kayan alatu da yawa.

Ba ya son gado ko kujerun zama masu kwalliya da lankwashe- lankwashe kuma ya fi son launuka masu duhu masu sauki ga idanuwa.

Yana da matukar alfanu ki rika la’akari da haka lokacin gyara da tsarin dakunan kwana da hutawarku.

’Yin tsari da kwalliya daidai irin nafsiyyar namiji zai sai maigida nishadi kuma ya samar masa da hutun ma’aikatar hankali.

Kila hakan ya sa maigida ya rika fita hirar dare ko zaman majalisa.

Dubarun nuna kauna daga dakin girki: Wani karin magana na Turawa na cewa hanyar shiga zuciyar namiji shi ne ta tumbin cikinsa.

Wato in uwargida ta gyara cikin maigidanta ta hanyar ciyar da shi dadadan abinci, to tsaf za ta samu wurin zama a zuciyarsa.

To haka abin yake, kowane maigida na jin dadin abinci mai dadi da matarsa ta dafa.

Amma mu sani, dadin abinci kadai bai samar da soyayyar namiji sai an hada da kulawa, kyautatawa da kuma ladabi da biyayya.

Wasu ’yan dabarun daga madafar abinci da uwargida za ta yi wanda za su kara dandanon zamantakewar aure:

Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano