Ramadan: Tsakanin daukar nauyin tafsiri da ciyarwa wanne ya fi falala?
Yayin da wasu malaman suke ganin ciyarwa ta fi falala, wasu kuwa sun ce daukar Tafsirin ya fi muhimmanci.
A daidai lokacin da ake shirin fara Azumin bana, hankali ya fara karkata kan mutane marasa karfi da yadda za su gudanar da Azumin.
Aminiya ta ruwaito a makon jiya yadda marayu da aka kashe musu iyaye a harin ’yan bindiga da sauran masu gudun hijira za su kasance cikin Azumin. Sai muhawarar da aka dade ana yi ta shin tsakanin ciyar da mabukata da daukar nauyin tafsiri wanne ya fi?
Hakan ya sa Aminiya ta zanta da wasu malamai domin jin ta bakinsu akan wannan batu.
Ciyar da mabukata a Azumi ya fi muhimmaci a kan daukar nauyin Tafsir – Sheikh Halliru Maraya
Aminiya ta zanta da fitaccen malamin nan, Sheikh Halliru Maraya, inda ya ce a yanzu a Najeriya an yi kiyasin akwai talakawa da ke rayuwa kasa da Dala daya sama da miliyan 80 a fadin kasar wadanda kuma suna fama da yunwa.
Sheikh Maraya ya bayyana cewa daukar nauyin karatuttuka na da muhimanci. Shi ma domin hanya ce ta isar da sakon Allah, sai ya ce idan har mutum na da halin ciyarwa tare da daukar nauyin tafsirin baki daya, to yana da kyau kuma idan an yi hakan lada ne mai yawa mutum zai samu.
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne ciyar da talakawa a raba su da yunwa. Shi ne ya fi musamman kasancewar halin da Najeriya ke ciki a yanzu wanda muke da mutane sama da miliyan 80 da ke cikin tsabagen talauci.
“Saboda haka halin da Najeria ke ciki babu abin da ya fi da ya wuce a taimaki talakawa duk da cewa daukar karatuttuka na da muhimmanci, amma idan mutane na cikin yunwa ai karatun ma ba za su fahimce shi ba,” inji shi.
“Kiran da zan yi a nan shi ne masu dukiya su taimakawa talakawa musamman ’yan uwansu na kusa sannan makwabtansu sannan sauran talakawa. Amma idan abubuwa sun hadu a lokaci guda ana so a yi su amma kudaden ba za su isa ba, sai a dauki wanda ya fi muhimmaci kuma a wannan hali abin da ya fi muhimmanci shi ne taimakawa mutane a rage musu radadin talauci. Mutum ya yi Azumi, lokacin shan ruwa ya yi ba shi da abin buda baki ba karamin tashin hankali ba ne,” inji shi.
Adawa suke yi da yada kalmar Allah – Sheikh Mansur Sakkwato
A nasa jawabin, Sheikh Farfesa Muhammad Mansur Ibrahim, wanda aka fi sani da Sheikh Mansur Sakkwato ya bayyana wa Aminiya cewa daukar nauyin tafsir din ne ya fi.
A cewarsa, “Gaskiyar magana ba cewa na yi gara a dauki nauyin tafsiri da a ciyar ba, muhawarar da aka yi, takan taso shekara-shekara kan me ya sa masu kudi ke daukar nauyin sanya tafsirai a kafofin yada labarai bayan ga mutane mabukata masu jin yunwa?
“Abin da zai ba ka mamaki shi ne shekarar bara ba a yi tafsiri ba, mafi yawa Najeriya, masu wannan yekuwar ba su ce komai ba kan a taimakawa talakawa, asalin muhawarar ta taso ne wajen mutanen da damuwarsu da adawarsu don me ake yada kalmar Allah a watan Azumi.
“Ramadan watan Alqur’ani ne don a lokacin aka saukar da Qur’ani, tun Qur’ani bai gama sauka ba duk shekara Mala’ika Jibril sai ya sauka a wajen Manzon Allah (SA.W) su yi tafsirin Qur’ani su tattauna da sauransu, a lokacin da Qur’ani ya cika sau biyu suka yi tafsiri a watan Azumi.
“Ka ga wata ne na tafsiri da ake son ma’anonin Qur’ani su isa ga mutane. Masu daukar tafsirin suna yi ne domin su isar da kalmar Allah ga jama’a, in ka bincika su ne ke ciyarwa da taimakon al’umma don me wani zai ce bai kamata a yi wannan ba, bayan lokaci gare shi, da ciyarwa da duk wani akin taimakon jama’a kamata ya yi su karu in Azumi ya zo amma bai kamata su soki wani aiki na addini ba.
“In ba watan Azumi ba, da wuya ka samu inda ake tafsiri sai ka je makaranta amma watan yini gaba daya ana gudanar da shi. Haka Abdullahi Danfodiyo ya yi a lokacin da ya je Kano.
“Akwai bukatar karantar da mutane a Azumi in ba ka sanya karatu a kafar sadarwa ba, me za ka sa? kade-kade da wasanni? Ba mu ce a daina aikin alheri ba a watan Azumi sabanin masu muhawarar da so suke yi a daina tafsiri gaba daya, ko ba a ciyar ba, in aka daina hankalinsu zai kwanta.
“Amma ni na tafi kan a tafi da su gaba daya, masu hali su yi gaba daya domin kowanne nada nasa muhimmanci.”
Malam ya kara da cewa, “bari na nemo maka abin da na ce; a shafina na Facebook na yi maganar ‘Cewa ciyarwa ta fi karantarwa ba sabuwar magana ba ce, mun saba jinta kuma mun san manufarta, musu kin su ji karatun Alqur’ani a watan azumi za su mutu da bakin ciki’ ka ga a nan ban ce kada a ciyar ba, manufar maganar su hana tafsiri duk masu wannan magana. Burinsu fada da tafsiri, shi ne asalin muhawarar.”
Da Aminiya ta tambaye shi kai tsaye a cikin ciyarwa da tafsiri wane ne ya fi a watan Azumi, sai ya ce, “Kaddara kana son maganar fifiko, da za ka tambaye ni Malam ina da dubu 300 shin in ciyar da mutane a watan Azumi ko na Dauki nauyin darasi na awa Daya tafsiri a sanya a Rediyo, zan ce ka dauki nauyin darasin.
“Dalili kan haka ko ka ba mutane abinci ko ba ka ba su ba sai sun nemo shi, karantar da Qur’ani abincin da zukata ke bukata ne a cikin watan azumi an fi bukatar wannan. Don haka gara ka ba mutane abincin ruhi sama da na jiki, duk mai hankali zai ce gara ka ba su abincin ruhi.
“Su dai malamai a kowane watan Azumi suna kira sosai a taimakawa bayin Allah, matsalar ita ce al’ummarmu ta yanzu taimako ya yi karanci cikinta, zuciyar rahama da tausayi ta yi karanta a cikin mutane, duk da bai kamata mu rufe ido ga abin da ke gudana na alheri da yawan attajirai ba, wasu na taimakawa har gwamnati tana yi, bai kamata mu raina kadan da ake yi ba.”
‘Abin da mutane suke cewa’
Aminiya ta zanta da Kwamared Aminu Abdullahi, inda ya bayyana cewa, “Idan kika duba mutane na fama da yunwa a gefe daya kuma ga tsadar kayayyakin abinci. Idan aka samu masu kudi suka rubanya ciyarwar da suke yi ta hanyar soke daukar nauyin tafsirai da suke yi abin zai amfanar domin Allah ne kaxai Ya san yawan mutanen da za su ci abinci daga wannan ciyarwa.”
Shi ma wani dan gwagwarmaya, Kwamared Abdussalam Tijjani ya bayyana cewa kudin da ake daukar nauyin tafsiri ya fi wanda ake ciyar da mutane a watan Ramadan.
“Wani abin dariyar ma shi ne za ki ga wani tafsirin na malami daya amma sai ki ga an sanya shi a kusan dukkanin gidajen rediyo da ke jihar nan. Kuma idan kin duba yawancin malaman nan abu daya suke maimaitawa. Abin da nake nufi idan akalla mutum ya ji na wani malamin ya wadatar masa ba za a ce koyaushe sai ya ji na dukkanin malamai ba.
“Ba wai muna cewa kada a sa tafsiri ko daya a gidajen rediyo ba. A nan wasu masu kudin su dauki nauyin tafsirin wasu kuma su juyar da akalar kudin ga bangaren ciyarwa domin al’umma su samu su yalwata a wannan wata mai albarka.”
Shi kuwa kuma Malam Hussaini Alhassan ya bayyana cewa kowane da matsayinsa.
“Kowa ya san idan ana maganar yunwa ba a maganar komai. Amma idan ya kasance mutum yana da wadata zai iya yin gaba dayan , ma’ana ya ciyar da mabukata ya kuma dauki nauyin tasfirin. Alhamdu llilah. Wanda kuma yawancin mutanne da ke daukar nauyin tafsiran nan za ka samu suna ciyarwa da mabukata a wanann lokaci.
“Kuma shi batun abinci ya danganta da bukatar mutum a yanzu haka wani ya samu abincin amma sai ki ga saboda halin rashin wadatar zuci da muke da shi sai ki ga yana hangen zuwan wani abincin daga wani waje. Wannan ba daidai ba ne.”