Ramadan: ’Yan kasuwa ku saurari wannan
Bahaushe ya yi gaskiya da yake cewa shekara kwana ce, hakika wannan karin magana ta yi daidai da wannan zamani da muke ciki, ganin yadda wuni da kwana sun zama kamar kiftawar ido, duniya tana gudu cikin gaggawa kamar walkiya, wannan kuwa ba wani abu ba ne illa alamun zuwan duniya karshe. Mutane suna kwana, […]
Bahaushe ya yi gaskiya da yake cewa shekara kwana ce, hakika wannan karin magana ta yi daidai da wannan zamani da muke ciki, ganin yadda wuni da kwana sun zama kamar kiftawar ido, duniya tana gudu cikin gaggawa kamar walkiya, wannan kuwa ba wani abu ba ne illa alamun zuwan duniya karshe. Mutane suna kwana, suna tashi, ba tare da sun ankara ba za su riski shekara ta kuma zagayowa, ni kaina abin ya zo mini da bazata, domin kuwa ina ganin kamar ba a fi wata ukku da gama azumin ramadan na shekarar 1433, wadda ta shude ba; sai ga shi yau din nan ‘yan kwanaki kadan suka yi saura domin shiga cikin azumin watan ramadan na shekarar hijirah ta 1434 ga wadanda Allah ya dara wa rana domin gabatar da ibada.
Sanin kowa ne cewa azumi wata babbar ibada ce kuma wajibi ce ga dukkan musulmi, yana cikin cika-cikan musulunci guda biyar, Allah (s.w.a) da kansa ya yi mana umarni da azumtar watan ramadan kamar yadda ya zo cikin kur’ani inda Allah yake cewa: “ya ku wadanda sukayi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi akan wadanda suke daga gabaninku, tsammaninku, za ku yi takawa” (al-bakara; 183). Watan Ramadan wata ne da yake da falala da ni’imomi masu tarin yawa, a cikinsa ne Allah yake ‘yanta dubban bayinsa daga wuta zuwa aljannah, a cikinsa ne Allah yake wanzar da daren lailatil-kadari, yawan falalar da take tattare a watan ramadan Allah ne kadai yasan abinsa.
Babban jan hankalin da nake son yi ba zai wuce ga masu hali daga cikinmu da kuma ‘yan kasuwa ba. Marrar da ake ciki a yanzu ta kai hatta lokacin azumi masu rayuwar hannu baka hannu kwarya a cikin al’umma rayuwarsu ba ta sauya zane wajen cin su da shan su, sanin kowa ne ya kamata a ce duk yadda mutum ya kai da talauci ya rinka samun sauyin abinci lafiyayye a lokacin azumin ramadan domin a wadannan lokuta jiki ya fi bukatar abinci mai rai da lafiya domin samun sukunin gabar da ibadarsa cikin annushuwa. Amma abin takaici sai ka ga talaka ya kai azumi abin da zai sanya a bakin salatinsa ma na neman ya gagare shi, mai gata shi ne za ka samu koko da kunu sai kosai da zogale, daga dan lemu sai kankana da dan ruwan sanyi a gabansa. Kuma duka wannan baya wuce irin halin talauci da ake fama da shi a cikin kasa ba, na tabbata duk wanda ya kai azumi zai so ace ya samu abinci lafiyayye kuma mai dadi da mando irin na makulashe ba jigari-jigari ba, sai dai da yawa mutane suna yin maleji ne kasancewar nan ne Allah ya ajiye su kuma babu yadda suka iya.
Kamar kowace shekara idan ta zagayo ana samun wasu ‘yan tsiraru daga cikin masu hannu da shuni wadanda suke kwadayin rahama daga wajen mai duka wadanda suke tashi tsaye suna antayar da dukiyarsu wajen bada agajin abinci ga marasa karfi, domin su masu wadata su kuma ci alfarmar ramadan. Kamar kullum muna kara karfafawa irin wadannan mutane gwiwa da su ci gaba da irin wannan taimako da suke yi, su sani cewa duk abin da suka yi Allah yana linka musu shi ne linkin-ba linkin kuma za su warbi romon abin ranar da dukiya ko ‘ya’yan ba za suyi aiki ba.
Ta bangaren ‘yan kasuwar mu kuma musamman manyan diloli wallahi akwai kalubale mai tarin yawa a tare daku, nasan mutane za su yarda dani idan nace lokacin azumi idan ya zo kayan masarufi suna tashin gwauron zabi, abin da zai baka takaici shi ne idan kaje shago yin sayayya za ka samu abin da za ka saya farashinsa ya daga daga lokacin da ka saye shi a lokacin da ba azumi ba. Idan ka tambayi mai shago yaya haka take faruwa? Zai ce maka ai ba laifinsu ba ne su ma a farashi mai tsada aka sayar musu, to wai manyan ‘yan kasuwa mene ne dalilinku na yin haka a lokacin azumi? Rashin kishin watan ne ba ku yi? Ko rahama ce ba kwa so? Ko kuma burinku kawai ku kuntatawa al’umma? Muna bukatar amsar wadannan tambayoyi daga gare ku.
Sannan muna kara baku shawara da kuji tsoron Allah, domin wallahi duk shekara idan lokacin azumi ya kewayo sai mutane sun yi korafi kan yadda kayan suke tashin gwauron zabi, kuna saka mutane cikin kunci da damuwa. Akwai mutanen da suke yin sayayyar azumi tun kafin karasowar watan suna yin haka ne domin su kaucewa irin tsadar rayuwa da za su samu kansu a ciki a lokutan azumin. Allah Ya ba mu sa’ar gabatar da wannan ibada lafiya Allah ya sa muna cikin wadanda zai ‘yanta a cikin
wannan wata mai alfarma.
A karshe ina son yin amfani da wannan dama in mika ta’aziyya ta ga Kamfanin Media Trust, game d arasuwar Manajan-Edita Malam, Suleiman Muhammad, muna rokon Allah ya dube shi da idon rahama ya kyautata makwancinsa ya sanya aljannatul’firdaus ta zama makoma a gareshi AMEEN.
Ibrahim IBB Kazaure 07031616267 ko 08183908615.w