Ramadan: ’Yan kasuwa sun yi alkawarin daidaita farashin kayan abinci
Kungiyar ’yan kasuwar Arewa ta yi alkawarin fallasa masu boye kayan abinci
Kungiyar ’yan kasuwar Arewa ta Najeriya (ATAN) ta yi alkawarin hada kai da daukacin mambobinta na Abuja domin daidaita farashin kayan abinci a watan Ramadan.
Sabon shugaban kungiyar na Abuja, Alhaji Habib Muhammad-Gajo, ya yi wannan alkawarin ne a jawabinsa ranar Talata a Abuja.
Gajo, ya bayyana shirin kungiyar na hada gwiwa da Hukumar babban birnin da kuma Gwamnatin Tarayya don bankadowa da kuma hukunta masu boye kayan abinci.
Wannan, a cewarsa, “zai yi kawo daidaito da kuma saukin farashin kayayyakin abinci a Abuja da ma kasa baki daya.”
- Yunwa ta sa ‘yan Najeriya cin ganye —Kungiyar kwadago
- Har yanzu ba a ba mu mulkin kamo Ado Gwanja ba — ‘Yan sanda
Tun da farko, shugaban kwamitin amintattu na kungiyar na kasa, Dakta Abdulaziz Bature, ya bukaci shugabannin kungiyar da su ba da jagoranci da ake bukata a yunkurin kungiyar na shawo kan matsalolin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta.
Ya kuma jaddada bukatar hadin kai da kuma tafiya da kowane bangaren ’yan kasuwa a babban birnin kasar nan.
A nasa jawabin shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Ibrahim Muhammad ya bukaci sabbin shugabanin da su gudanar da mulki na bai daya.
“Kwazonku, iya aiki da amincinku da ya ba ku wannan mukami, na yi imanin zai zaburar da ku wajen samar da ingantaccen shugabanci, kuma mun san kuna da jajircewa wajen neman ’yancin da kuke jagoranta.
“Muna fatan wannan gajeren wa’adin da za ku yi na watanni shida zai kawo kyakkyawan ci gaba ga mutanen Abuja.“