Ramadan: ’Yan Nijar sun rage kudin burodi a Bauchi

Shugaban kungiyar Al’ummar Nijar mazauna Jihar Bauchi Alhaji Mainasara Moussa ya bayyana cewa kungiyarsu ta ba da umarni ga mambobinsu su rage farashin kudin burodi albarkacin wannan wata na azumin Ramadan. Shugaban kungiyar Alhaji Mainasara Moussa shi ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Bauchi a ranar Litinin da ta gabata.Alhaji […]

Ramadan: ’Yan Nijar sun rage kudin burodi a Bauchi
Ramadan: ’Yan Nijar sun rage kudin burodi a Bauchi

Shugaban kungiyar Al’ummar Nijar mazauna Jihar Bauchi Alhaji Mainasara Moussa ya bayyana cewa kungiyarsu ta ba da umarni ga mambobinsu su rage farashin kudin burodi albarkacin wannan wata na azumin Ramadan.

Shugaban kungiyar Alhaji Mainasara Moussa shi ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Bauchi a ranar Litinin da ta gabata.
Alhaji Mainasara ya ce watan azumi wata ne da Allah Ya umarci Musulmi ya yi azumi matukar yana cikin koshin lafiya, sai ya shawarci ’yan kasuwa su rage farashin kayan masarufi kamara shinkafa da sukari da man girki da kayan marmari.
Alhaji Mainasara ya ce daga cikin wadanda suka rage farashin kayayyakinsu sun hada da masu sayar da burodi da masu tsire da masu sayar da shayi.
“Domin duk wanda ya tausaya wa mai azumi shi ma Allah zai tausaya masa kuma za mu ci gaba da ba da shawarwari ga ’yan kasuwa kan wannan mataki,” inji shi.
Sai ya shawarci malamai masu tafsiri a masallatai su daina sukar juna a yayin da suke karantar da al’umma, domin yin haka ba zai haifar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi ba.