Ramadan: Za mu kwace lasisin duk wanda ya kara farashi —BUA
Kamfanin ya yi alakwarin kwace lasisin dilansa masu kara farashin kaya n don kuntata wa al’umma
Kamfanin kayan abinci na BUA ya ce zai kwace lasisin duk wani dilan kayansa da ya kara farashin kayan don kuntata wa al’umma da neman kazamar riba a watan Azumin Ramadan.
Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Abdussamad Isiyaku Rabiu ya ce kamfanin ya riga ya samar da kayan da za su wadaci abokan huldarsa a fadin Najeriya a watan na Ramadan da ma bayansa, kamar sukari, taliya da fulawa da sauransu.
- Tafsirin Ramadan: Izala ta tura malamai 500 zuwa kasashe
- Ya fille wa kakarsa kai, ya kai ofishin ’yan sanda
- Ramadan: Hanyar magance sabanin ganin wata —Farfesa Mansur
- Damfara ta miliyan N450 aka yi rana guda —Ummi Zee-Zee
“Ina ba ku tabbaci cewa muna da kaya a ma’ajiyarmu da za su wadaci Arewacin Najeriya, da suka hada da tan-tan na sukari a Sharada da zai wadacii jama’ar Kano, Kebbi, Jigawa, Yobe, Maiduguri, Zamfara da Katsina.
“BUA na kuma tabbatar muku cewa ba zai kara farashin kayansa a cikin watan Ramadan ko bayansa ba,” inji Abdussamar ta bakin Wakilin Kamfanin mai Kula da Yankin Arewacin Najeriya, Muhammad Adakawa cewa.
Ya jaddada cewa kamfanin ba zai raga wa duk wani abokin huldarsa da ke son fakewa da karuwar bukatan mutane na nau’ikan kayan da kamfanin ke samarwa yana kuntata musu ba a watan Ramadan.
“Mutane ba su sani ba, amma yawanci masana’antu ne suke kara farashin kayansu a watan Ramadan, amma ina kyautata zaton da wannan abun da kamfanin BUA ya yi, bana ba za a samu karin farashi ba,” inji shi.
Adakawa ya roki Gwamantin Tarayya da rage harajin da take karba daga kamfanoni masu shigo da kaya daga ketara, wanda a cewarsa, hakan zai taimaka wajen saukaka farashin kayan da ake shigo da su daga kasashen waje.