Ramadaniyya: Kyautar musamman ga mai azumi (3)
An karbo daga A’isha (RA) ta ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana I’itikafi a kwana goma na karshen Ramadan har ya bar duniya.”21. Zakkar fidda kai:Zakkar fidda kai ita ce zakkar da ake yi idan aka gama azumi. An ce ta halatta kafin a gama azumi da kwana uku ko biyu ko daya ko ranar […]
An karbo daga A’isha (RA) ta ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana I’itikafi a kwana goma na karshen Ramadan har ya bar duniya.”
21. Zakkar fidda kai:
Zakkar fidda kai ita ce zakkar da ake yi idan aka gama azumi. An ce ta halatta kafin a gama azumi da kwana uku ko biyu ko daya ko ranar daren Sallah ko ranar Sallah kafin a je masallaci. An samu Hadisi daga dan Abbas (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya wajabta mana Zakkar fidda kai don tsarkake mai azumi daga miyagun maganganu da kura-kurai. Kuma ciyarwa ce ga talaka. Wanda ya ba da ita kafin a je masallacin Idi ya samu ladar zakka, Wanda ya ba da ita bayan dawowa daga Idi, yana da ladar sadaka ne kawai.” Abu Dawud ne ya ruwaito.
Ita Zakkatul Fitir (Zakkar Fidda-kai) tana kan maigida ne da wadanda suke karkashinsa kamar matansa da ’ya’yansa da ma’aikatansa da sauran wadanda suke karkashinsa maza da mata na Musulmi kuma ana ba da ita kafin fita zuwa masallacin Idi.
22. Lokacin Sallar Idi:
Za a iya gabatar da Sallar Idi daga lokacin da rana ta fito ta dago sama, wato lokacin da shari’a ta yarda a yi sallar nafila har zuwa lokacin da rana za ta kai tsakiyar sama, ko tsakiyar zafinta.
23. Wurarin da ake sallar Idi:
Wurin da ya kamata a yi sallar Idi shi ne filii kamar hamada ko fako ko filin da ba ginanne ba. Za a iya yin sallar a wani wuri idan hamadar za ta iya yin illa ko wurin yana da cabi ko ruwa ya kwanta. Manzon Allah (SAW) yana gabatar da sallar Idi a kan yashin hamada. Masallacinsa ya fi hamadar, amma duk da haka yakan bar masallacin ya tafi hamadar. Wannan wata Sunnah ce mai karfi. Matukar babu wata lalura a yi sallar Idi a wajen gari baya ga wadanda suke Harami a Makka. Malamai sun ittifaki cewa sallar Idi a fili ya fi lada a kan yi a ginannen masallaci. Abu Sa’idul Khudri ya ce: “Manzon Allah (SAW) yakan je filin Baki’a (wani fili a wajen Madina) don ya gudanar da Sallar Idi.” Buhari da Muslmi suka ruwaito. Don haka a Makka ne kawai aka yarda a gabatar da sallar Idi a cikin masallacin Harami. Kuma yayin gabatar da sallar Idi ba a yin kiran Sallah ko ikama. Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Ba a kiran Sallah kafin Sallar Idi.” Buhari da Muslim suka ruwaito shi. Jabir (RA) ya ce: “Ba a kiran Sallah ko ikama yayin Sallar Idi.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Imam Malik ya ce: “Wannan shi ne koyarwar Manzon Allah (SAW) kuma babu wata jayayya a kai.”
24. Yawan kabbarori yayin Sallar Idi:
Sallar Idi raka’a biyu ce. A raka’ar farko liman da mamu a bayan ya fada za su yi kabbarori bakwai a bayyane. Wadannan kabbarori bakwai ba su hada da kabbarar harama (ta farko) ba. Dagan an sai liman ya yi karatun Sallah, Fatiha da Sura wadanda ake karantawa a bayyane. Raka’a ta biyu kuma kabbarori biyar bayan kabbarar tasowa daga raka’ar farko.
25. Azumin da ake so mutum ya rika yi bayan na Ramadan:
a. Azumi shida a watan Shawwal: Saboda Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya yi azumin watan Ramadan kuma ya yi shida a watan Shawwal, za a ba shi ladan wanda yya shekara yana azumi.
b. Azumin Litinin da Alhamis: Saboda Annabi (SAW) yana yawaita yin azumi a ranar Litinin da Alhamis, sai aka tambaye shi, yaya kake yawaita azumi a ranar Litinin da Alhamis, sai ya ce, a ranakun ne ake daukar ayyukan bayi zuwa ga Allah.
c. Yin azumi uku kowane wata: Ranar 13 da 14 da 15 ga wata, kuma suna da lada kamar mutum ya yi azumin shekara ne. Domin duk wani aikin alheri za a ba ka lada goma.
d. Azumi tara a Zul-Hajji: Ana son mutum ya yi azumi tara a watan Zul Hajji har da na Ranar Arfa ga wanda bai mai aikin Hajji ba.
e. Azumin Tasu’a da Ashura: Wato azumin ranar tara da goma ga watan Muharram watan daa na Musulunci.
26. Azumin da aka hana yi:
a. Azumi rana kokwanto, wato ranar 30 ga watan Sha’aban alhali ba a ga jinjirin wata ba, dalili shi ne ba a sani ba Ramadan ake ciki ko Sha’aban. Saboda wannan shakka aka hana yin azumi a wannan ranar.
b. An hana yin azumi ranar Idi, karamar Sallah ko Babba. An ruwaito Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda ya yi azumi a ranar Idi ya saba wa Baban kasim (Annabi SAW don yana da da mai suna kasim, shi ya sa ake yi masa alkunya da Baban kasim).
c. An hana azumi bayan Sallah da kwana daya zuwa kwana uku.
d. An hana kebe ranar Juma’a ita kadai da yin azumi.
e. Bai halatta ga mace ta yi azumin nafila ba sai da izinin mijinta.
27. Nasihohi zuwa ga masu azumi:
dan uwa Musulmi ka yi aiki da wadannan nasihohi:
1. Ka yi azumin watan Ramadan kana mai imani da Allah kuma ka kyautata shi don a gafarta maka laifuffukanka da suka gabata.
2. Kada ka yarda ka karya azumin watan Ramadan da gangan don yin haka yana daga cikin manyan laifuffuka.
3. Kuma ka tashi tsaye don yin Sallar Tarawihi, musaman a goma karshe wadanda ake samun daren Lailatul kadari wanda Allah Ya ce a kansa: “Alherin da ke cikin Daren Lailatul kadari ya fi watanni dubu.
4. Ka yi kokari abincinka da abin shanka su zamo halal, don a karbi ayyuka da addu’o’inka. Kada ka yarda ka yi azumi sannan ka yi buda-baki da haram.
5. Ka yi kokari ka ba wani abin buda-baki ko ya yi buda-baki da abincinka don ka samu lada daidai da ladan azuminsa.
6. Ka tsare salloli a kan lokaci tare da jama’a don ka samu ladar jam’i kuma Allah Ya tsare ka daga masifar rayuwa.
7. Ka yawaita sadaka domin sadakar da ta fi lada ita ce sadakar da ka yi a cikin watan Ramadan.
8. Ka yi kokari ka yi sahur, idan so samu ne ka yo hakuri zuwa karshen dare kafi ketowar alfijir. Allah Yana sanya albarka a cikin Sahur.
9. Ka gaggauta buda-baki da zarar rana ta fadi, don ka samu yardar Allah.
10. Ka yi kokarin wankan janaba in ka sadu da iyalinka a cikin daren azumi don ka samu yin Sallah cikin tsarki da jama’a.
11. Ka dukufa ga karatun Alkur’ani a cikin Ramadan don ya zama hujjarka ba hujja a kanka ba, kuma ya zamo mai cetonka ranar kiyama.
12. Ka tsare harshenka kada ka la’anci wani ko ka zage shi ko ka yi gibarsa. Kuma ka tsare idonka da kunnenka daga gani ko jin abubuwan haram da lagawu kamar wake-wake da kade-kade. Sannan ka tsare hannunka daga sata ko daukar kayan daba naka ba, ko cutar da wani da shi. Haka ka tsare kafarka daga zuwa inda Allah Ya hana. Azumi ba hana ci da sha ba ne kawai hard a kamewa daga duk abin da Allah Ya hana.
13. Ka yi kokari ka danne zuciyarka ka guje wa fadace-fadace da zage-zage. Ka ji tsoron Allah a fili da boye. Da yawaita tuba da neman gafara da rokon Aljanna da duk wani alherin duniya da Lahira ga kanka da iyayenka da sauran al’ummar Musulmi.