Ramalan Yero ya samu tikitin takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Arewa a APC

Yero ya yi gwamnan Kaduna tsakanin shekarar 2012 zuwa 2015 bayan rasuwar tsohon gwamna, Patrick Yakowa.

Ramalan Yero ya samu tikitin takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Arewa a APC

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya lashe zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Kaduna ta Arewa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC.

An bayyana Yero a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya samu ƙuri’u 6,060, inda ya doke Muhammad Mu’azu Mukaddas wanda ya samu ƙuri’u 1,044 da kuma Yusuf Bala Ikara wanda ya samu 372.

Jami’in gudanar da zaɓen, Hassan Saleh, ne ya sanar da sakamakon yau Litinin a Zaria.

Yero ya yi gwamnan Kaduna tsakanin shekarar 2012 zuwa 2015 bayan rasuwar tsohon gwamna, Patrick Yakowa, a hatsarin jirgin sama.

Da yake jawabi bayan zaɓen, Yero ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana, tare da kira ga sauran ’yan takarar su haɗa kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a Zaɓen 2027.