Ramin da ake tonon kasa ya rufta a kan almajirai hudu
Wani rami da ake tono kasa ya rufta da wasu almajirai hudu a Tattarawa da ke ya karamar Hukumar Dawakin Tofa a ranar Alhamis din makon jiya inda nan take almajiran suka rasu sakamakon danne su da kasar ta yi. Da yake yi wa wakilinmu bayani, malamin almajiran Malam Lawan baure, ya ce almajiran su […]
Wani rami da ake tono kasa ya rufta da wasu almajirai hudu a Tattarawa da ke ya karamar Hukumar Dawakin Tofa a ranar Alhamis din makon jiya inda nan take almajiran suka rasu sakamakon danne su da kasar ta yi.
Da yake yi wa wakilinmu bayani, malamin almajiran Malam Lawan baure, ya ce almajiran su biyar ne suka fita yawo da yammacin ranar, bayan sun dawo ne sai suka bi ta wajen da ake tonon kasar, sai hudu suka shiga cikin ramin suka bar cikon na biyar yana fitsari daga waje.
Malam Lawan baure ya ce kafin daya almajirin ya gama fitsarin ne sai ya ji fuftawar ramin inda nan take ya garzaya wajen masu tifar da suka bar wurin bayan sun debi kasar ya sanar da su cewa rami ya rufta kan ’yan uwansa, kuma nan take suka koma suka tono yaran wadanda Allah Ya yi masu rasuwa kafin a tono su.
Malam Lawan baure duk shekara yana zuwa garin Kwa domin ci rani inda a karshe ya yi gidan kansa yana koyar da karatu a makarantarsa ta allo da ke Layin Dole a garin Kwa.
Ya ce kafin yaran su fita sai da ya umarce su da su yi aski saboda sumar su ta yi yawa. Ya ce Allah cikin ikonSa sai suka sayi reza suka tafi da ita inda kafin su shiga ramin suka yi wa juna aski.
Tun a yammacin wannan rana ta Alhamis ce aka yi jana’izar almajiran inda dimbin jama’a suka halarta. Kuma almajiran da lamarin ya rutsa da su sun hada da Kabiru Ahmed daga Burum-Burum ta karamar Hukumar Rano da Samawilu da Hassan Idi da Nasiru Nasara dukkansu daga Burdudu ta karamar Hukumar baure a Jihar Katsina.