Ramuwa
Wani malami ne yana koyar da dalibansa karatu, sai ya tada wani dalibi ya ce masa: “Goma a tara da goma.” Yaron ya ce bai sani ba sai ya falla masa, ya ce masa: “Ashirin ke nan, ka haddace idan ba haka ba, ba za ka yi ilimi ba.” Ana cikin karatu sai malamin ya […]
Wani malami ne yana koyar da dalibansa karatu, sai ya tada wani dalibi ya ce masa: “Goma a tara da goma.” Yaron ya ce bai sani ba sai ya falla masa, ya ce masa: “Ashirin ke nan, ka haddace idan ba haka ba, ba za ka yi ilimi ba.” Ana cikin karatu sai malamin ya ce ko akwai mai tambaya, sai wannan dalibin ya daga hannu ya ce: “Malam tambayata ita ce: “Idan ka ga Naira duba daya da kuma wata Naira dari biyar a kasa, wacce za ka dauka?” Malam ya ce Naira dubu daya zai dauka. Yaron ya daga hannu ya falla wa malam mari, ya ce: “Nan gaba idan ka gansu duka za ka dauka, idan ba haka ba talauci zai kasha ka.”
Iliyas Idris Fahad Suleja