Ramuwar gayya: ‘Yan fashi sun kashe mutum 50 a kauyen Kizara
…..Sun yi wa Sarki da Limamin garin yankan rago A makon da ya gabata ne mutanen kauyen Kizara da ke karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara suka gamu da fushin ‘yan fashi lokacin da suka auka musu har suka kashe sama da mutum hamsin, ciki har da Limamin garin,wanda suka yi wa yankan rago, suka […]

…..Sun yi wa Sarki da Limamin garin yankan rago
A makon da ya gabata ne mutanen kauyen Kizara da ke karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara suka gamu da fushin ‘yan fashi lokacin da suka auka musu har suka kashe sama da mutum hamsin, ciki har da Limamin garin,wanda suka yi wa yankan rago, suka dauki Alkur’ani suka dora masa a kirjinsa, suka kuma kama hakimin garin, shi ma suka yi masa yankan rago shi da wadansu mutane.
Yadda abin ya faru kuwa shi ne, da asubahin ranar Talata din wannan makon ne wadansu ‘yanfashi dauke da bindigogin da ke sarrafa kansu suka kewaye kauyen Kizara da ke karamar Hukumar Tsafe, wadanda aka ce sun je ne su yi ramuwar gayya, suka kuma samu nasarar kashe sama da mutane hamsin, ciki har da mace guda da yara guda biyu.
Su dai wadannan ‘yan bindigan ba su dauki komai ba a gidajen jama’a, sai wadansu babura da aka ce sun tafi da su na wadanda suka kawo dauki kuma suka samu nasarar kashe su. Wannan ramuwar gaiyar ta biyo bayan kama wadansu barayi su uku ne da ‘yan bangan kauyen suka yi kuma har suka gutsere wa guda daya hannu, sannan suka mika su ga jami’an tsaro.
Wannan matakin da ‘yan bangar suka dauka ya sa su ‘yan fashin suka aiko da sakon daukar fansa, wanda hakan ya sa Gwamnatin Jihar Zamfara ta kai jami’an tsaro ta jibge, amma tun lokacin da aka kai jami’an tsaron babu abin da ya faru, sai bayan an dauke su da kwana uku, kuma rundunar ‘yansanda ta dauke su ne don a canza su, sai dai ba a yi saurin tura wadansu ba har hakan ya faru.
Alhaji Lawalli shi ne uban kasar Kizara wanda barayin suka yi wa yankan rago, sai kuma Limamin masallacin garin mai suna Malam Labbo Usman, shi ma sun yi masa yankan rago suka kuma dauki Alkur’ani suka dora masa a kirji, sai kuma wani dan banga mai suna Garba Buda wanda da farko suka kasa kashe shi sai suka rabka masa gora a kai, wani kuma ya tokare shi ya fadi sannan suka yi masa yankan rago.
A halin da ake ciki yanzu dai cikin garin Kizara an kashe mutum 31, ciki har da mace guda mai suna Saratu, tare da wadansu yara guda biyu, a kauyen Gobirawa kuwa da suka kawo dauki an kashe mutum biyar, sai garin danjibga da su ma suka kawo dauki an kashe mutum biyar, sai wani gari da ake kira Yarzega inda aka kashe mutum hudu, sai Sabon garin Dutsen Kura da ke da mutum biyu da aka kashe, sai wani gari mai suna Unguwar gero da su ka rasa mutum biyu, sai Hummuri da suka rasa mutum daya, sai ‘Yarnasarawa da ta rasa mutum daya.
Sai dai bayan kammala jana’izar mutanen, wakilinmu ya samu labarin an kawo wadansu daga asibiti su kusan mutum hudu, wadanda suka mutu daga baya. Sai dai wata majiya ta bayyana cewa, sai bayan da wadansu suka bar garin suka rasu. Kusan kimanin garuruwa goma sha biyar ne abin ya shafa, a sakamakon kawo dauki da suka yi.
Malam Rabi’u daya ne daga cikin wadanda suka kawo dauki, ya bayyana wa wakilinmu cewa, suna ji, suna gani suka kasa karasawa garin, domin makaman da barayin suke dauke da su manya ne, don karansu kawai ya ishe ka, kuma daga baya ma kabbara suka dinga yi suna kiran jama’a su fito. Ya kara da cewa, ‘’ko kana da makami babu abin da za ka iya yi, domin barayin sun fi dari da hamsin.’’
Wata kuma mai suna Zainab Abu da wakilinmu ya same ta za su yi gudun hijira, ta bayyana cewa, da misalin karfe uku na dare mutanen suka shigo, amma ba su shigo garin ba sai da asubahi, wani wuri ma sun gama sallarsu. Ta ce ba ta taba ganin tashin hankali irin wannan ba, ta ce su yanzu kam ba za su koma garin ba, don sun samu labarin an kashe kusan mutum 48 zuwa lokacin da wakilinmu yake zantawa da ita.
Idris Keta tsohon dan majalisar wakilai ne mai wakiltar Gusau da Tsafe, a zantawarsa da wakilinmu ya dora laifi ne kacokan a kan Gwamnatin Tarayya, don a cewarsa, babu yadda za a yi a ce gari kamar Kizara a turo masu dan sanda guda daya kawai babu ko bindiga, alhali garin yana dauke da mutune sama da dubu biyar, don haka babu wanda ke da alhakin kashe wadannan mutanen sai Gwamnatin Tarayya.
Mai martaba Sarkin Tsafe Alhaji Habibu Aliyu ya yi wa jamaar garin jawabi, inda ya bukaci su dauki hakuri domin duk abin da Allah Ya shirya sai ya faru, kuma babu wanda yake mutuwa sai kwannansa ya kare, ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka rasu.
Kwamishinan ‘yansanda na jihar Zamfara Usman Arkilla Gwari, a zantawarsa da manema labarai a garin Kizara ya tabbatar da faruwar wannan al’amarin kuma ya ce kimanin mutum 38 ne suka mutu, kamar yadda suka samu bayani , kuma ya bayyana cewa za su sauya ‘yan sandan da suka dauke kamar yadda sukayi alkawari, kuma ba za su bar garin ba sai sun gabatar da wadanda za su bari a garin , kuma ya tabbatar da cewa wannan harin ramuwar gayya ce suka zo suka yi, kuma za su ci gaba da daukar mataki.
A ranar Alhamis din makon jiya ma wadansu ‘yan fashi da ba a tantance yawansu ba sun yi wa wadansu sojoji da ‘yan sintiri kwanton-bauna inda suka harbe sojoji biyu da ‘yan sintiri biyu a kauyen Kwasa-kwasa da ke yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Cikin sojojin da suka rasa rayukansu har akwai wani mai mukamin Laftanar. ‘Yan fashin sun samu nasarar kashe sojojin da ‘yan sintirin ne a lokacin da suke alwala domin gudunar da sallar asubahi da misalin karfe biyar na asubahi. Haka kuma cikin wadanda suka rasa ransu akwai farin kaya mutum biyu.
Irin wannan kashe-kashen ya zama ruwan dare a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna, inda a jihar Zamfara a ranar 11 ga watan Agustan shekarar 2011 ‘yan bindiga suka kashe mutum 19 a kauyen Lingyado, a kuma watan Fabrairun shekarar 2012 suka kashe tare da kona mutane 15 a Birnin Magaji, a watan Oktoban shekarar 2012 kuma suka kashe mutum 27 a dangulbi, a watan Nuwamban shekarar 2012 kuma suka kashe mutum 20 a kauyen Kabaro.
A jihar Katsina kuma ‘yan bindigan sun kai farmakin garurruwan Fankama da Unguwar Tsamiya da Unguwar Maigora .
A jihar Kaduna kuma ‘yan fashin sun addabi yankin Birnin Gwari ne, inda suka kai hari a a watan Oktoban shekarar 2012 suka kashe mutum 20 a cikin masallaci a garin Dogon Dawa, a cikin watan kuma sun kashe ‘yan sanda guda uku a garin Birnin Gwari, a watan Yunin shekarar 2013 kuma sun kashe mutum 7 a Goron Dutse kuma kwanan nan suka kashe mutane shida a wani farmakin da suka kai kauyen Kwasa-kwasa, cikin wadanda suka kashe har da soja da dan sanda.
……Sai an yi amfani da jiragen sama za a magance matsalar – Musa Zubairu
Daga Mohammad Yaba, Kaduna
Wani kwararre a fannin tsaro da ke Kaduna, Malam Musa Zubairu ya bukaci gwamnatin jihar da kuma rundunar ‘yan Sanda su yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen gano maboyar ‘yan fashi da suke addabar al’ummar yankin Birnin Gwari.
A cewarsa, wannan ita ce hanya daya da za a iya kawo karshen yawan halaka bayin Allah da ‘yan fashin ke yi a yankin.
Malamin wanda masani ne fannin aikata laifuka (Criminology) da yake da kamfanin harkar tsaro, ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya ta wayar tarho, inda ya nuna cewa dole ne sai jami’an tsaro sun yi amfani da jama’ar yankin wajen tattara bayanan sirri domin yaki da wadannan ‘yan ta’addan.
“Tun da gwamnati ta ce tana sayan jiragen sama masu saukar ungulu ya kamata a rika amfani da su domin binciken dazuzzukan da ke wannan yanki. Jiragen ba an saye su domin a kare masu mulki ba ne, an saye su ne domin kare mutanen kasa. Don haka akwai bukatar yin amfani da su wajen yakar bata-garin nan da ke damun al’ummar yankin,” inji shi.
A game da cewa akwai karancin jami’an tsaro, Malamin sai ya ce,” Muna da ‘yan sanda kusan sama da dubu 400 ne a kasar nan amma kusan dubu 100 da ‘yan kai suna aiki ne na daukar jakunkunan manyan mutane da kuma kare su. Ta yaya za a yi su isa? Idan ka dubi wadannan abubuwa da ke faruwa za ka ga cewa akwai takaici. Saboda haka akwai bukatar a gyara wannan matsala in dai ana son a inganta tsaro a kasar nan. Bayan haka kuma jami’an tsaro su rika gyara yadda za a yi jama’a su rika ba su bayanan sirri kuma a yi amfani da bayannan yadda ya kamata. Kuma kada idan mutum ya kai musu rahuto su zama masa dodo,” inji shi.
Malam Musa ya kuma ce idan har ba a samun bayanai masu kyau daga wajen mutane zuwa ga jami’an tsaro ba dole a rika samun matsalar rashin tsaro. Wanda hakan ya sa dole sai an rika amfani da jiragen sama a wannan yanki na Birnin Gwari za a samu nasarar korarsu daga yankin.
“Bayan haka akwai bukatar talakawa su yarda da jami’an tsaro wajen ba su bayanai da za su taimaka wajen yakar bata-gari a wannan yankin. Mutanen yankin babu yadda za a ce ba su san bata-garin nan ba, amma saboda akwai rashin yarda a tsakanin talakawa da jami’an tsaro dole a rika samun matsala a yankin. Ko a kasashen turawa talakawa ke saka ido, musamman ga duk bakon da ya shigo masu unguwa ko gari,”inji shi.
Ya kuma bukaci gwamnati da jami’an tsaro su tabbatar da sun fito da wani tsari na inganta tsaro a wannan yanki da zai taimaka wajen kawo karshen wannan al’amari da ya ki ci, ya ki cinyewa.
Daga karshe ya bukaci a kara yawan jami’an tsaro a yankin in dai ana bukatar samun nasara wajen fatattakar ‘yan fashin daga yankin.