Ranar Asabar Gwamnatin Katsina za ta aurar da mutane 2000
A wata sanarwa da kwamitin shirya bikin ɗaurin auren ya fitar, za a yi bikin ɗaurin auren a ƙofar gidajen Hakimai
A gobe Asabar 9 ga watan Mayu, 2026 za a yi bikin aurar da mutane 2000, maza 1000 mata 1000 kamar yadda Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi alƙawali.
A wata sanarwa da kwamitin shirya bikin ɗaurin auren ya fitar, za a yi bikin ɗaurin auren a ƙofar gidajen Hakiman waɗanda za a aurar.
- Sojoji ba su da abin yi a kafafen sada zumunta — Rundunar Soji
- Sojoji sun bindige ’yan ta’adda 3 a Zamfara
Daurin auren wanda ya zamo irin shi na farko da gwamnati ta ɗauki nauyi ya fi mayar da hankali ga zawarawan da suka rasa kodai mazajen su ko matayen su sanadiyar iftila’in hare-haren ’yan bindiga.
Daurin auren zai kasance da misalin ƙarfe 10 na safe a ƙofar gidajen Hakiman da ke faɗin ƙananan hukumomin jahar 34.
Akwai ƙarin bayani nan gaba.