Ranar da Halifan Shata ya tsuma dattawa a Katsina
A ranar 10 ga watan Janairun bana, kungiyoyin masoya Dokta Mamman Shata Katsina suka shirya taron karrama marigayin, inda suka kaddamar da dan autansa, Sanusi Shata a matsayin Halifan Shata. Taron dai ya yi armashi, inda ya samu halartar dimbin matasa da dattijai da masu binciken tarihi da suka yi nazari da wallafe-wallafe kan marigayi […]
A ranar 10 ga watan Janairun bana, kungiyoyin masoya Dokta Mamman Shata Katsina suka shirya taron karrama marigayin, inda suka kaddamar da dan autansa, Sanusi Shata a matsayin Halifan Shata.
Taron dai ya yi armashi, inda ya samu halartar dimbin matasa da dattijai da masu binciken tarihi da suka yi nazari da wallafe-wallafe kan marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron, akwai Alhaji Sani Zangon Daura da Sa’in Katsina Alhaji Ahmadu Na-Funtuwa da Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Katsina, Dokta Kabir Matazu da Alhaji Surajo Mai Asharalle, wanda ake wa lakabi da ‘Garkuwan Mamman Shata.’
Sanusi Mamman Shata ya fara cashewa tun kimanin karfe biyar na yamma har zuwa magariba, inda Sa’in Katsina ya ce, to a tashi a je a yi Sallah. Sannan aka dawo bayan Sallar Isha’i, Halifa ya yi ta rera wakokin Shata da kuma sabuwar wakar Sarkin Bauchi, Alhaji Lurwanu Adamu. Tsofaffi wadanda suka dade da sanin Shata, wadannan wakoki sun tsuma su.
Su kuwa makadan Shata suna cikin kidi, sai aka ji kidan kamar ya yi kasa, nan da nan Dokta dankwari ya bayyana wa jama’a cewa, ganga daya ce kadai ke motsi. Don haka aka tuntubi makadan Shata, sai aka ga Nuhu Babanyara yana kuka, shi yasa ya bar kidan.
Shi kuwa Sa’idu Sasuwai cewa, ya yi wata sa’a idan suna yi wa Sanusi kida yana waka sai su rika ganin mahaifinsa, saboda kamar da dan ya yi da mahaifinsa.
A bangaren matasa kuwa, Malam danjuma Katsina da Dokta Lawal Musa dankwari da Dokta Ali Ibrahim kankara, wadanda suka shahara a wajen bincike da wallafa makaloli da littattafai kan rayuwar wannan mashahurin mawakin, duk sun halarci bikin.
A wajen wannan taro, Autan Shata ya cashe, inda ya rera wakokin mahaifinsa, ya kuma yi nasa sababbi. A jerin wakokin da ya yi, sun hada da wakar Sarkin Bauchi Lurwanu Sulemanu Adamu. Sannan ya rera wa Sarkin Dass waka.
Makadin Shata Alhaji Sa’idu Sasuwai, wanda ya buga masa kidan Bakandamiya da wakar Alhaji Sarkin Zazzau Shehu, ya roki marubuta da masu bincike kan tarihin Shata da su yi taka-tsan-tsa, saboda a cewarsa, “tarihin Shata daji ne, abin da aka yi da kai ko wanda aka yi da shi ya bayyana maka, shi ne za ka tabbatar. “An yi karairayi da yawa a kan Shata, wasu na cewa an ji kida ranar da aka haifi Shata, to wane shege ne ya yi kidan? A da in mun tafi Funtuwa, in dare bai yi ba, to sai in wuce Filato. To, ka ga idan ba ni nan aka zo, aka dauke shi zuwa Sakkwato, duk abin da aka yi ban sani ba. Saboda haka ku ’yan jarida ku rika yin bincike kafin ku buga hirar mutum da hotonsa,” inji Sasuwai.
Shi kuwa Nuhu Babanyara, makadin Shata, cewa ya yi ya ji dadin zama da Marigayi Dokta Mamman Shata Katsina. A cewarsa: “Shata dai yana da abu daya, in yana son ka, yana son ka, ba wai zai duba abin da za ka ba shi ba. Dominj mafi yawan wadanda ya yi wa waka ba kudin ne suka sanya ya yi musu ba.
“Mun zauna da Alhaji, mun bi shi kuma ya nuna mu. Saboda haka in Allah Ya yarda daga nan har mu koma inda ya tafi, za mu ci arzikinsa. Sai dai ni abin da nike jin tsoro game da ’yan jarida shi ne, in na kera allura sai a ce na kera garma.”
A wajen wannan taro, Dokta Lawal dankwari Malami a Sashen Harsunan Najeriya da ke Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, ya yi matukar yaba wa jaridar Aminiya, inda ya bayyana cewa, ya dade bai sayi jarida ba, amma da Aminiya ta bullo da hira da wadanda Shata ya wake sai ya fara saye.
“Shekara biyar ke nan ban sayi kowace irin jarida ba, duk da cewa ina rubutu na musamman a kan Dokta Mamman Shata sama da shekara 10. Kai tun marigayi na raye nike bibiyar harkokin rayuwarsa, amma da Aminiya ta fara hira da mutanen Shata, sai na koma sayen jarida. Kuma na dade ban fita daga gidana ba, bayan Sallar Isha’i, amma yau saboda Shata ga shi mun wuce karfe 10,” inji shi.
Dokta dankwari, wanda masani ne a harshe da adabin Hausa, ya yi takaddama da Dokta Ali Ibrahim kankara, wanda a halin yanzu ya fi kowane marubuci yawan makaloli da shirye-shirye a kafafen yada labarai da ya dade yana yi a kan Shata. Takaddamar masanan an yi ta ne a kan wakokin Shata biyu, wadanda suka hada da ta Indon Musawa da Idi Na-Tajo Maisaniya. Masannan sun yi ittifaki a kan cewa, Alhaji Idi Na-Tajo Maisaniya, wanda Aminiya ta wallafa hirarsa da hotonsa, tabbas shi ne, amma ita Indon Musawa masanan sun samu sabani, inda Dokta dankwari ya ce akwai Indon Musawa ta gaskiya, wadda ya dauke tawagar mahalarta taro tare da Halifan Shata da makadansa aka je gidan Indon Musawa ta gaskiya; kusan kowa ya ce ita ce. Sai dai wani abin mamaki, wadda Aminiya ta buga hirarta, Dokta Ali Ibrahim kankara ya ce lallai akwai, kuma kamar yadda ta bayyana wa Aminiya, hakika ta matsa wa Shata lallai sai ya yi mata waka; kuma sunanta Indon Musawa.
Da aka kammala taro da bikin kaddamar da Halifa Sanusi Mamman Shata, sai kowa ya waste, baki kuma suka tafi masauki. Washegari, sai ’yan kungiyar masoya Dokta Mamman Shata karkashin jagorancin Dokta Lawal Shehu dankwari suka dunguma sai gidan Sa’in Katsina, Alhaji Ahmadu Na-Funtuwa, wanda ya tarbi baki, ya kuma yi musu jawabin godiya da neman afuwa, musamman ma ganin cewa, bai samu damar komawa filin wasa ba, bayan Sallar Isha’i; inda ya ta’allaka al’amarin da ‘tsananin sanyi.’
Daga nan sai ya bayar da labarin wata takaddama da suka yi da Alhaji Mamman Shata, inda ya bayyana cewa: “A lokacin rayuwar marigayin, ya ce sai ya ba ni haushi, ni kuwa na ce, ba za ka iya ba ni haushi ba, tunda an ce a wannan zamanin da wuya a samu wani mawaki mai hazakarka.
“Wata rana bayan na manta da cewa, Shata ya yi nufin ba ni haushi, sai kawai ya ce da ni ka sanar da mutane cewa, ‘yau zan fasa kwai.’ Ni kuwa sai na sa aka bude Nasara Kulob, mutane suka yi ta biyan kudinsu, domin Shata ya ce zai fasa kwai. Nan da nan kuwa wuri ya dinke. Muka taru, amma har karfe 10 na dare Shata bai zo ba. Sai wani mutum ya zo ya ce mana me kuke jira, muka ce Shata, sai ya ce, watakila Shata yanzu ya kai Daura. Sai na tambayi mutumin a ina ka gano shi? Shi kuwa ya ce na gan shi a Muduru. Ni kuwa ina jin haka, sai na dauki mota, sai Muduru.
“A can na same shi yana barci a cikin daji kuma yaransa sun kewaye shi. Ina shiga sai na yayimi gadon, na saka shi a cikin mota muka yi ta gudu. Na gargade shi da cewa, idan har ka sake ka ce za ka fito, to karairayewa za ka yi. Na kawo shi Katsina, yaransa suka biyo shi. Da muka iso sai ya roke ni, in kyale shi ya je gidan Uwar Bayye ya sauya kaya, tunda wadancan na bata su. Da ya kimtsa ya fito sai da ya kwana yana wasa,” inji Sa’i.
A cewar Sa’i, wata rana kuma sai Alhaji Mamman Shata ya bayyana mini cewa, so ya yi a kakkarya kujerun nan na Nasara Kulob masu tsada. Ni kuwa na ce masa, Allah Ya yi ba ka ba ni haushi ba.”
Da kamala jawabin Sa’in Katsina, sai mahalarta wannan taro suka yanke ranar wani bikin, don su gabatar da Halifa a birnin Daura, cikin wata mai kamawa, amma sai Sa’in Katsina ya bayar da shawarar cewa:
“A daga taron har sai Allah Ya kai mu watan Yuni, domin a cikinsa muka rasa Alhaji Dokta Mamman Shata Katsina. Aranar 19 ga Yunin 19999 Allah Ya yi wa Alhaji Shata rasuwa, don haka ina ganin zai fi kyau a dage wannan har sai ranar ta zagayo.”
Don haka daukacin ’ya’yan kungiyar da suka ziyarci gidan Sa’in Katsina sun tafi a kan cewa, sai Allah Ya kai rai za sake yin taro na musamman a kan Dokta Alhaji Mamman Shata Katsina.