Ranar da Shata ya yi min waka kewaye ni aka yi ana kallo – Abashe Mai hoto

“Mai hoto Abashe yaro,  Ko daga zuci ya dau hotonka,In ya je gida zai wanke,  Mai hoto Abashe yaro.”  Alhaji Abashe Mai hoto na daya daga cikin wadanda marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina ya yi wa waka a lokacin rayuwarsa. Alhaji Abashe shi ne Bahaushen farko a Katsina da ya fara sana’ar daukar hoto tun […]

Ranar da Shata ya yi min waka kewaye ni aka yi ana kallo – Abashe Mai hoto
Ranar da Shata ya yi min waka kewaye ni aka yi ana kallo – Abashe Mai hoto

“Mai hoto Abashe yaro,  
Ko daga zuci ya dau hotonka,
In ya je gida zai wanke,  
Mai hoto Abashe yaro.”
 
Alhaji Abashe Mai hoto na daya daga cikin wadanda marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina ya yi wa waka a lokacin rayuwarsa. Alhaji Abashe shi ne Bahaushen farko a Katsina da ya fara sana’ar daukar hoto tun ana Jihar Arewa ta Tsakiya. Aminiya ta gana da shi don jin yadda ya hadu da Mamman Shata har ya wake shi:

Aminiya: Ko za mu ji takaitaccen tarihinka?  
Abashe Mai hoto: Ni Alhaji Abashe Mai hoto, lakabin da ake kirana shi ne ’Yar’aduwa, to amma ni mutumin kofar Guga ne, a can aka haife ni. A takaice ina da shekara sittin da dan wani abu yanzu. Na yi karatun addini a Zariya a lokacin Sarki Jafaru yana da rai. Bayan na gama karatu a Zariya sai na bi wani yayana yana aiki a Ma’aikatar Ayyuka (M.O.W) muka yi ta ’yan yawace-yawace da shi, inda muka zauna a Kaduna da Zariya da Jos da Kabba da Kagoro. To daga can ne muka rabu da shi domin yawon ya ishe ni. Tunda ban yi ilimin boko ba, sai na ga ya kamata in koyi sana’a. To sai shi yayan nawa ya tambaye ni irin sana’ar da nake so. Sai na ce, daukar hoto. Sai ya ce, “Me ya sa kake son sana’ar hoto? Ka san babu wasu Hausawa ciki duk kabilu ne.” Na ce, ni dai shi nake so domin akwai gudunmawar da zan bayar. Na farko, akwai tafiya aikin Hajji, akwai Lena, akwai Lasin da sauran abubuwan da duk sun shafi hoton nan. Saboda haka, kamata ya yi, in zamo Bahaushe na farko da zai zamo mai daukar hoton don in taimaki ’yan uwana har in koya wa wasu. Da haka ya yarda na fara aikin hoton a Jos. Na yi wata shida da farawa sai aka maido shi Kagoro, a nan ma aka hada ni da wani mai hoton mutumin Rukuba. A nan na yi wata hudu na samu satifiket na kuma ce babu inda zan zauna sai Katsina. Na taho lokacin da ake gab ga Yakin Basasa. Ana zanga-zanga Ibo na yin Kudu ni kuma na yiwo Katsina. Lokacin da na zo kantin Ibo masu daukar hoto biyu ne. To kantin Joliwulda na shiga domin shi ya tafi. Nan na ci gaba da daukar hoto a halin yanzu shekara ta 46 ina daukar hoto.  
Aminiya: Mene ne musabbabin wakar da Shata ya yi maka?
Abashe Mai hoto: Musabbinta an fara yakin Najeriya mu da Biyafara, to ka san sojoji sukan zo hutu in sun samu kudi sukan yi shagali. Akwai wani Kanar na manta sunansa, shi ya zo da Shata kantina ya ce, yana so a yi masa hoto kuma wannan lokaci yake so a wanke a ba shi yana so zai koma Enugu. Nan take na dauke shi hoto na je na wanke na kawo masa. To ka san wancan lokacin in an dauki hoto yau sai gobe ake zuwa a karba. Ba tare da Shata na dauke su ba, amma ganin yadda na yi, ya sa Shata ya tambaye ni ko ni Bahaushe ne? Na ce masa ni Bahaushe ne. Sai ya tambaye ni inda na koyi daukar hoto, na ce masa Kagoro. Ya yi ta dai yi mani tambayoyi ina ba shi amsa.  
Aminiya: A lokacin ka gane ko shi wane ne?  
Abashe Mai hoto: kwarai kuwa! Na san Shata ne. To bayan ya gama yi mani tambayoyin sai na ce
masa, ba mu kananan ’yan kasuwa ba, manyan kamfanoni suna neman sabo da kai. Sai ya ce mani, “Kada ma ka ce komai. Akwai kaya da Yunibasiti (Jami’a) suka ba ni, zan sanyo su in zo ka dauke ni hoto.” Ni kuma sai na ce masa,”To tun daga yau kana bina bashin hoto.” Sai da aka yi shekara biyu duk inda na gan shi sai na tuna masa cewa har yanzu yana bina bashin hoto ban biya ba. Ran nan sai aka yi sa’a akwai wani wasan gargajiya da za a yi A nan Katsina bayan an yi na Kaduna. Shata ba ya cikin wadanda aka sanya a cikin shirin saboda shari’ar da suke yi da Sarkin Musawa akan wakar Gagarabadau, to amma saboda kwarjininsa da ya je sai aka sanya shi. To shi Shata yana da wani abu, duk inda za a yi wasa sai dai a sanya shi a karshe domin daga gare shi wasa ya tashi koda kuwa da shi aka fara budewa. To a nan ne fa na je na dauke shi hotuna daban-daban kashi 12. Wasu shi kadai wasu kuma cikin mutane. Kafin Shata ya gama wasa,nan da nan na zo gida na wanke hotuna kati 12 na sa gilashi na kai masa gidan Hajiya Bayye inda ya sauka na aza a bisa gadonsa na yi tafiyata. Lokacin da ya zo da farko fada ya fara yi a kan wanda ya ajiye masa hotuna a bisa gado. To amma da ya duba sai ya ce, ya san maganar, wato na biya bashi. To daga nan ne ya fara wakar,”Yaya ka yi ka dau hoton nan? Shin daga zucci ka dau hotan nan sai da ka je gida ka wanke?” Har yana cewa, “Koda zamanin yin yaki ka san ba a taba mai hoto ba, to raba ka dau hotonka. Duk da Amerika da ke hoto, duk su ma Abas ya san su.” Ya yi mani wannan wakar ce a 1973.  
Aminiya: To Alhaji Abashe daga cikin wakar da Shata ya yi maka, wadanne baitoci ne da ko ranka ya baci in ka tuna su za ka ji dadi?  
Abashe Mai hoto: Akwai inda yake cewa,”Koda zamanin yin yaki ka san ba a taba mai hoto ba, rarraba ka dau hotonka. Duk da Nasara suka yo hoto, duk sun san Abas ya sansu.” Akwai inda yake cewa, “Abas dama ka koma Legas, wai sai na ce masa,”ni Katsinarmu birnin Dikko ’Yar’aduwarmu nan zan zauna, duk mai so in dau hotonsa, to ’Yar’aduwa ya zo ya ishe ni.”  Akwai dai kalmomi da dama wadanda ya yi mani. Kuma in dai Hausa ce, ka ji kalma tsantsa, to sai Shata.   
Aminiya: To, ranar farko da ya yi maka wakar yaya kaji?   
Abashe Mai hoto: Ba ma ji ba, kewaye ni aka yi ana kallo.   
Aminiya: An ce muddin Shata ya ce yana son abu za a ba shi ko ba a yi niyya ba, haka ne?    
Abashe Mai hoto: To ni dai tunda nake ban taba ba Shata kudi ba, sai dai yaransa domin su ne ke sa ya yi maka waka in suna sonka. Su yake tambaya a kan wakar da ya yi, to in suna so duk inda kuka hadu ya maimaita sai su ce, ai jama’a na sonta, in kuwa suka ce, ai jama’a tafiyarsu suke yi, sai ya ce, ashe aikin banza muke yi. To baya kara yin wannan wakar. Amma da zarar sun ambace ka, to ba ya tashi sai ya yi maka waka. Kuma a gaskiya, samun mawaki ya yi waka ta amsa sunanta sai Shata. Ai shi da kansa ya ce, a batun mawaka babu kamar mutum uku. A yi waka ta tarihi sai Mamman Sarkin Taushin Katsina, a yi waka kamar yanzu za a yaki sai Narambada, a yi wakar da za a kira waka sai Shata.