Ranar da uwargidana ta rasu

Ta rasu da magribar daren Juma’a, lokaci mai falala. Ta samu shaida mai kyau daga wajen mutane da yawa.

Ranar da uwargidana ta rasu

Ana ta cece-kuce gameda wanda ya kamata ya fara gaida wani tsakanin miji da mata

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa amin.

Ga ci gaban bayani a kan rabuwa da abokiyar aure don Ma’aurata su kara hakuri da juna da kau da kai ga kurakuran juna, su zauna koyaushe cikin aminci da juna.

Sannan su rika saurin yafiya da mance laifi don ko da ta kasance Allah Ya kaddara rasuwar daya daga cikinsu, a rabu cikin amincin ba cikin jin haushin juna ba.

Allah Ya Jikan Ummu Muhammad Zarewa, shekara 6 bayan hukuncin Allah.

A ranar Laraba 19/4/2017 baiwar Allah ta je daukar hoton ciki Makarfi sai dai an samu abin daukar hoton yana da matsala, kasancewar ina Zaria wajen aiki sai na ce mata ki taho da safe sai mu hadu mu je wani asibitin.

Ta zo Zariya ranar 20/4/2017, na tarbe ta cikin fara’a da wasa da dariya irin ta miji da mata, na kaita inda za ta ci abincin safe, kasancewar ina da taro a safiyar sai na hada ta da wani aboki dan’uwa na jini ma’aikacin jinya domin ya dauki hoton cikin nata a asibitinsu na musamman da ke gefen Zaria.

Ashe ajalinta a hannunsa yake, domin bayan ya dauki hoton, ya ga haihuwarta za ta kama ranar 27/4/2017, sai zuciyarsa ta ba shi shawarar ya yi karambani, ya dankara mata allurar jawo nakuda, saboda tsarin da ya karanta na cewa haihuwa tana iya zuwa kafin sati biyu ko bayan sati biyu na lokacin da aka yi hasashe a ilimin kimiyya.

Bayan mun gama taro, sai na tafi don na dauko ta, bayan mun fito sai yake ce min ya yi mata allurar nakuda fa za ta iya haihuwa yau.

Na duba takardar da take hannuna sai na ga 27/4/17 za ta haihu, sai na yi nazarin yinin da muke ciki sai na ga 20/4/17, na san Ummu Muhammad nakudarta ba ta wuce minti (30), sannan kuma ga asibiti kusa da Zarewa, sai na ce mu koma gida, in ma ta tashi sai mu tafi asibiti mafi Kusa.

Mun koma Zarewa da ‘yan awanni sai nakuda ta taso, na kira mahaifiyarta, muna shirin tafiya asibiti sai wancan ma’aikacin jinyar ya tura min wani yaronsa, wanda a hannunsa kaddara ta faru, inda bayan ya ciro dan, uwa ta dare biyu.

Ummu Muhammad ta waigo inda nake sai ta ce min Sheikh mutuwa zan yi, ka yafe min abin da na yi maka, na mayar da abin wasa, kasancewar tana cikin hayyacinta, kuma ba ta tagayyara ba.

Na sake shigowa inda take, sai ta sake maimaita min, “Sheikh ka yafe min, in na mutu ka kaiwa IYA yarana kar ka ba wa matarka.”

Na tuna shekarun da muka yi tare, dole akwai kurakurai, “na yafe miki, ni ma ki yafe min”, sai ta ce: Na yafe maka Sheikh, ba ni ruwa na sha”, shi ke nan ta yi shiru sannan ta cika.

Ina tuna Ummu MUHD da barkwancinta, mutuwarta abar tada hankali ce, sai dai akwai abubuwa guda (7) da suke saukaka Damuwa:

1. Na yi shekara guda Ina mafarkin mala’ikan mutuwa yana zuwa min ziyara, yakan zaro raina har sai ya kusa fita sai ya bar ni ya tafi. Bayan ta rasu bai sake zuwa ba. Wannan sai ya nuna hukuncin ne tsararre daga Allah.

2. Ta rasu bayan mun yafe wa JUNA, wanda hakan yana cikin karamomi masu girma. Za ka tara ma’aurata guda 1,000 ba ka samu biyu da haka ta faru ba.

3. An yi min haihuwa har guda 7, amma ba a taba yi min haihuwar da na kasa sayan kayan jarirai ba sai wannan.

Duk lokacin da ta ce min Sheikh ya kamata mu je kasuwa, mu hado kayan jarirai sai wata kasala ta buge ni, ba na iya ba da amsa, hakan sai ya nuna kaddara ta riga fata.

4. Abin da wancan Nurse din ya yi mata zai iya zama kaffara da daukakar daraja gare ta.

5. Ta rasu da magribar daren Juma’a, lokaci mai falala.

6. Ta samu shaida mai kyau daga wajen mutane da yawa.

7. Na yi mafarkin Ummu Muhammad tana zaune a wani katon gida, ta ci kwalliya da fararen kaya, tana rike da jaririnta, ni kuma ina kusa da ita, muna shan soyayya.

Allah Ya jikan Ummu Muhammad, Allah Ya shiryi ma’aikatan jinya masu karambani.

Mun kwafo wannan bayani daga shafin Sheikh Dokta Jamilu Zarewa Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin