Ranar Dimokuraɗiyya: ’Yan Najeriya a fusace suke da Tinubu — PDP
PDP ta ce babu abun a zo a gani da APC ta yi face jefa ‘yan Najeriya cikin tsaka mai wuya.
Jam’iyyar PDP ta zargi APC da jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali, inda ta ce jama’a a fusace game da halin da ƙasar nan ke ciki a halin yanzu.
PDP ta kuma yi iƙirarin cewa APC ta tozarta dimokuraɗiyyar da marigayi Cif MKO Abiola ya yi gwagwarmayar kafawa har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Debo Ologunagba, PDP ta buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da ranar dimokuraɗiyya ta bana don bayyana halin ƙunci da APC ta jefa ƙasar nan a ciki.
Kazalika, ta soki APC kan yadda ta keta kundin tsarin mulkin Najeriya, ta hanyar tafka magudin zaɓe, takurawa ’yan adawa da kuma yin zagon ƙasa ga tsarin shari’a a wani yunƙuri na mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.
Ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya yi tunani kan halin da al’ummar ƙasar nan ke ciki a ƙarƙashin mulkinsa, yayin da yunwa da tashe-tashen hankula ke ƙara ƙamari.
Jam’iyyar ta jaddada buƙatar shugaba Tinubu ya saurari ’yan Najeriya tare da sake duba manufofin da ke ƙara dagula al’amura a ƙasar nan.
Jam’iyyar ta koka da cewa maimakon a yi bikin samun ’yanci da shugabanci nagari, ’yan Najeriya na shan wahala sakamakon rashin aiwatar da manufofin da suka dace da APC ke yi.
PDP ta soki ƙarin farashin man fetur da wutar lantarki, inda ta ce jami’yyar APC ba ta samar da tsare-tsare da suka dace don inganta rayuwar jama’a ba.