Ranar Juma’a Buhari Zai Gabatar Da Kasafin 2023 Ga Majalisa

Shugaban Buhari zai gabatar da kasafin 2023 na Naira tiriliyan 19.76 ga Majalisar Dokoki ta Tarayya a ranar Juma’a 5 ga Oktoba, 2022.

Ranar Juma’a Buhari Zai Gabatar Da Kasafin 2023 Ga Majalisa

Buhari a lokacin gabatar da kasafin 2022 a zauren Majalisar Tarayya. (Hoto: Fadar Shugaban kasa)

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2023 na Naira tiriliyan 19.76 ga Majalisar Dokoki ta Tarayya a ranar Juma’a 5 ga watan Oktoba da muke ciki.

Sanarwar dai na kunshe ne cikin wata wasika da ya aika ga Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan, wacce ya karanta a zauren Majalisar ranar Talata.

Wasikar dai ta bayyana cewa Buharin zai gabatar da kasafin ne da karfe 10:00 na safiya, a zauren Majalisar Wakilai ta wucen gadi.

Shugaban Majalisar Dattijan ya ce tuni aka kammala shirye-shiryen karbar dukkan ’yan Majalisun da kuma ’yan rakiyar shugaban kasa.

Kamar dai yadda aka sani, yanzu haka ana ci gaba da gyare-gayre a Majalisar Dattawa da ta Wakilai, lamarin da ya sa ’yan majalisar suka koma matsugunin wucin gadi.