Auren zawarawa: Ranar Juma’a za a shafa Fatiha

Ranar Juma’ar wannan mako za a shafa fatihar auren gatan mutum 1,800 da gwamantin Jihar Kano ta dauki nauyi

Auren zawarawa: Ranar Juma’a za a shafa Fatiha

Gwamnatin Kano ta sanar cewa a ranar Juma’ar makon nan, 13 ga Oktoba za a daura auren zawara a karkashin shirinta na auren gata.

Gwamnan Abba Kabir ne ya sanar da ranar daurin aurne bayan ran gadinsa tsare-tsaren da Hukumar Hisbaha ta jihar ta yi domin daurin auren a ofishinta.

Mutum 1,800 ne za su ci gabajiyar auren gatan, wand suka hada da zawarawa da nakasassu da masu karamin karfi, daga kananan hukumomi 44 ta jihar, kamar yadda gwamnatin ta sanar.

Gwamnan ya yaba da yadda Hisbah ta yi tsarin, musamman ganin yadda auren gatan ya kunshi masu karamin karfi da kuma nakasassu.

Ya kuma yi alkawarin ba wa hukumar duk kulawar da ta dace, inda ya nuna bacin ransa da rashin kammala gine-ginen da  ke ofishin hukumar a tsawon shekaru takwas na gwamnatin da ta gabata.

Da yake jawabi, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce lokacin da aka dauki nauyin auren gatan da za a yi ya yi daidai, saboda ya kawo wa masu son aure sauki, sannan zai rage matsalar zinace-zinace.