Ranar Lahadi ce 1 ga watan Zul-Hijjah —Sarkin Musulmi

An bayyana ranar Lahadi a matsayin 1 ga watan Dhul-Hijjah.

Ranar Lahadi ce 1 ga watan Zul-Hijjah —Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci da ke Fadar Sarkin Musulmi, ta bayyana ranar Lahadi 11 ga watan Yuli, a matsayin ranar 1 ga watan Dhul-Hijjah, 1442 a Najeriya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar da yammacin Asabar.

  1. Allah Ya yi wa Sarkin Lafiagi Alhaji Sa’adu Kawu rasuwa
  2. Jarumin Kannywood Sani SK yana neman taimako

A ranar Juma’a ne dai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmin Najeriya da su fara duban watan Babbar Sallah na Zul-Hijjah daga ranar Asabar wanda ya yi daidai da 10 ga watan Yulin 2021.

Sarkin, wanda kuma shine Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, ya ce hakan ya biyo bayan ganin watan da aka yi a wasu sassa na kasar.

Watan Zul-Hijja dai shine wata na 12 a shekarar Musulunci wanda a cikinsa ne ake gudanar da bikin Sallar Layya da ma Aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Sai dai a bana ma kasar ta Saudiyya ta takaita adadin mutanen da za su gudanar da aikin hajjin zuwa 60,000 kacal, kuma suma dole su kasance mazauna cikin kasar saboda annobar COVID-19.