Ranar Lahadi ce 1 ga watan Muharram — Sarkin Musulmi

Yau Asabar ce 30 ga watan Zhul Hijja na shekarar 1445, sakamakon rashin ganin jinjirin watan Muharram a ranar Juma’a.

Ranar Lahadi ce 1 ga watan Muharram — Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar. (Hoto: Fadar Sarkin Musulmi)

Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya bayyana cewa gobe Lahadi ce za ta zama 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar Musulunci ta Hijira 1446.

Shugaban kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini, Farfesa Sambo Wali Junaid ne bayyana hakan a ranar Juma’a.

Farfesa Junaid ya ce kwamitin haɗin gwiwa da kwamitin ganin wata na Nijeriya sun tabbatar ba a samu ganin watan Muharram na shekarar 1446 a ranar Juma’ar ba, abin da ke nuna ranar Asabar za ta zama 30 ga watan Zhul Hijja na shekarar 1445.

“Sakamakon haka, Asabar [6 ga watan Yuni] ta zama 30 ga watan Zulhijja 1445…Lahadi kuma [7 ga Yuni] ta zama 1 ga watan Muharram 1446,” a cewar shugaban kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali cikin wata sanarwa.

“Sarkin Musulmi na taya Musulmin Nijeriya murna [sabuwar shekara] da kuma roƙa musu alheri da taimakon Allah,” in ji sanarwar.

Sarkin Musulmin ya roƙi jama’a su ci gaba da addu’ar zaman lafiya da samun ci gaba a ƙasa baki ɗaya.

A tsarin Musulunci, kowane wata kwana 29 ne amma idan aka kasa ganin jaririn sabon wata akan cika watan zuwa kwana 30.

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano

Ya kamata a kori shugaban INEC —Obasanjo