Kwallon kafa: Ranar Lahadi gwanayen Afirka za su fara artabu a Kamaru

Kasashe 24 ne za su fafata a wasanni 52 don samun kyautar $5m

Kwallon kafa: Ranar Lahadi gwanayen Afirka za su fara artabu a Kamaru

Allura cikin ruwa: Wa zai lashe Kofin Nahiyar Afirka? (Hoto: Twitter/@CAF_Online)

Ranar Lahadi za a bude Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta bana, inda gwanayen Afirka a taka leda za su yi artabu domin raba tsakanin tsaki da tsakuwa.

Gasar mai taken AFCON 2021, bara ya kamata a gudanar da ita, amma annobar Coronavirus ta hana.

Wannan ne karo na 33 da za a buga gasar, kuma kasar Kamaru ce mai masaukin baki, sannan Total Energy Africa ne zai dauki nauyinta.

Kasar Aljeriya ce ke rike da Kofin a halin yanzu, sannan kasar Misra ce ta fi kowace kasa lashe gasar, inda ta lashe sau bakwai.

A wasan farko, Kamaru ce za ta bude gasar da fafatawar da za ta yi da Burkina Faso a filin wasa na Olembe.

Binciken Bakin Raga ya gano cewa ba a doke kasar Burkina Faso ba ko sau daya a duk wasannin da ta buga na neman gurbin shiga gasar.

Sai dai a haduwar kasashen biyu ta karshe, Kamaru ce yi nasara.

An kara kudin gasar

A wani cigaba da aka samu, Hukumar Kwallon Afirka, CAF, ta kara kudin da ake ba zakarun gasar.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Kwamitin Zartarwa na Hukumar ta CAF ya zauna, inda ya amince da karin.

Shugaban Kwamitin Patrice Motsepe ne ya sanar da karin, inda ya ce tawagar da ta lashe gasar za ta samu kudi Dala miliyan 5, Karin $500,000 ke nan a kan kudin da aka ba Aljeriya da ta lashe gasar a wancan karon.

Tawaga ta biyu za ta samu Dala miliyan 2.75; kasashen da suka kai wasan kusa da karshe kuma za su samu Dala miliyan 2.2, sannan wadanda suka kai wasannin kusa da wasannin kusa da karshe za su samu Dala miliyan 1.175 kowannensu.

Filayen da za a buga wasannin

Za a buga wasannin a filaye shida.

Filayen su ne na Stade Omnisport Paul Biya, Olembe, inda za a bude gasar a birnin Yaoundé, sai Stade Ahmadou Ahidjo da ke Yaoundé, sai Japoma Stadium da ke Doula, da Limbe Omnisport Stadium da ke Limbe. da Kouekong Omnisport Stadium da ke Bafoussam da Roumde Adjia da ke Garoua.

Za a yi amfani da na’urar VAR

A karon farko, za a yi amfani da na’urar taimakon rafare ta VAR a Gasar Kofin Afirka a dukkanin wasannin gasar guda 52 maimakon na shekarar 2019 da aka fara amfani da na’urar daga wasannin kusa da na kusa da karshe.

Najeriya a gasar

Wasan Najeriya na farko

Ranar Talata ne Najeriya za ta buga wasanta na farko, inda za ta fafata da Misra.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi karo da tangarda a shirye-shiryenta na tafiya gasar, inda aka canja koci, sannan ta rasa manyan ’yan wasanta da ake sa ran za su taimaka mata sosai.

Daga cikin ‘yan wasa zarata da Najeriya ta so su buga mata akwai Victor Osimhen mai taka leda yanzu haka a kungiyar Napoli ta Italiya, wanda cutar Coronavirus ta hana zuwa.

‘Yan Najeriya suka yi zaton shi ne zai jagoranci gaban tawagar ta Super Eagles.

Sai dan wasan Watford ta Ingila, Dennis Emmanuel, wanda yanzu haka shi ne jigon kungiyar.

Kungiyar ta hana shi zuwa bisa dalilin cewa ba a tura mata wasikar nemansa ba a kan lokaci.

Akwai kuma Odion Ighalo, wanda shi ma aka bukaci ya dawo buga wa Najeriya kwallo bayan ya yi ritaya, amma kungiyarsa ta Al Shabbab ta Saudiya ta hana shi zuwa, bisa dalilin cewa a kwantiraginsu babu buga wa kasa wasa.

Sauran sun hada da Shehu Abdullahi da Leon Balogun da sauransu.

Ku kasance da shafin aminiya.dailytrust.com domin za mu bude shafi na musamman don kawo muku bayanai kai-tsaye (wato live blog) a kan wasan Najeriya na ranar Talata.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara