Ranar Litinin Kwankwaso da Obi za su bar ADC — Buba Galadima

Majiyar ta ce ana sanya hannu kan muhimman takardu domin komawar Kwankwaso da Peter Obi Jam’iyyar NDC

Ranar Litinin Kwankwaso da Obi za su bar ADC — Buba Galadima

Injiniya Buba Galadima, babban na hannun daman Sanata Rabiu Kwankwaso, ya sanar cewa Kwankwaso zai fice daga Jam’iyyar ADC a ranar Litinin. 

Buba Galadima, wanda shi ne Sakataren Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar NNPP, ya bayyana cewa a ranar Kwankwaso tare da abokin takararsa, Peter Obi, za su jagoranci magoya bayansu domin komawa sabuwar jam’iyya.

Ya sanar da haka ne a yayin tahon masu ruwa da tsaki na tafiyar Obi-Kwankwaso Movement a Abuja, wanda aka gudanar sakamakon fargabar rashin tabbas da hadakar jam’iyyun adawa ke ciki a game da zaben 2027.

Duk da cewa Buba Galadima bai bayyana jam’yyar da za su koma ba, Aminiya ta ruwaito cewa Obi da Kwankwaso, wadanda ke neman tikitin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a tare, suna shirin komawa Jam’iyyar NDC, wanda ake dangantawa da tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriaki Dickson.

Majiyoyi daga bangaren Kwankwasiyya sun sun shaida wa Aminiya cewa tattunawa tsakanin bangaren manyan ’yan siyasan biyu da Jam’iyyar NDC ta kusa kammaluwa.

Wata majiya ta bayyana cewa, “Obi da Kwankwaso da jagororin bangarorinsu sun halarci zaman da aka gudanar taun jiya, in da safiyar nan ake sanya hannu kan muhimman takardu tare da Sanata Seriaki Dickson da shugabannin NDC.”

Ta ci gaba da cewa, “Ba ma sa a maimaita abin da ya faru a ADC, inda muka lura cewa Atiku da magoya bayansu sun yaudari jagororinmu zuwa waccan jam’iyyar ce domin cimma muradi daya, ta takarar shugaban kasan Atiku.

“Yanzu komai ya kammalu. Obi da Kwankwaso za su sanar da komawarsu Jam’iyyar ADC a ranar Litini.

Wannan matakin da aka tsara ya biyo bayan makonni na hasashe game da inda Obi da Kwankwaso za su nufa a siyasa, musamman bayan sabbin hukuncin Kotun Koli da suka shafi jam’iyyun adawa da tsarin cikin gida na jam’iyyu.

Yayin da yake magana da ’yan jarida, Injiniya Buba Galadima ya gargadi magoya baya da su shirya don abin da ya bayyana a matsayin hare-hare da rikice-rikice da za su iya biyo bayan sanarwar.

Ya ce, “Daga Litinin, lokacin da shugabanninmu za su bayyana jam’iyyar za su tsaya, ina so in gaya muku cewa ɗaya daga cikin abubuwa biyu zai faru.

“Na farko, za su ɗauki hayar marubuta. Na biyu, za su tura masu tasiri a kafafen sada zumunta su fara kai wa ’yan takararmu hari. Duk wanda ke kan kafafen sada zumunta da sauransu, dole ne ku shirya don amsa duk abin da za su faɗa.

“Duk wani abu da za su iya faɗa game da shugabanninmu, waɗanda muka sani sosai a matsayin mutanen kirki da daraja, dole ne mu mayar da martani da ƙarfi kamar yadda ya dace da mutum mai basira.”