Ranar Litinin Makarantun Kano za su koma aji

Makarantun kwana za su dawo daga hutu ranar Lahadi na je-ka-ka-dawo kuma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.

Ranar Litinin Makarantun Kano za su koma aji

‘Yan makaranta mata a aji a Afghanistan

Makarantun firamare da sakandare a Kano za su koma aji ranar Litinin bayan ɗage ranar dawowarsu daga hutu da gwamnatim jihar ta yi.

Ma’aikatar ilmin jihar ta sanar cewa daliban makarantun kwana za su koma ranar Lahadi sannan su fara daukae darussa tare da takwarorinsu na makarantun je-ka-ka-dawo ranar Litinin 16 ga watan Satumba, 2024.

Sanarwar da Daraktan Wayar da Kan Al’umma na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Kiru, ya fitar ta bukaci iyaye da su tabbata ’ya’yansu sun koma makaranta kamar yadda aka tsara.

Sannan ya gargadi ɗalibai da su guji zuwa makaranta da makami ko duk wani abu da aka haramta.

Daga nan ya yi musu fatan alheri tare da malamansu a yayin da za su fara sabuwar shekarar karatu ta 2024/2025.

Da farko, ma’aikatar ta sanya 9 ga watan Satumba, 2024 a matsayin ranar dawowar hutun makarantun firamare da sakandare kafin daga bisani ta ɗage ranar, saboda wasu dalilai.