Ranar Litinin za a ci gaba da karatu a Jami’ar ABU

Za a sauya jadawalin karatun Jami’ar ABU na shekarar 2021/2022

Ranar Litinin za a ci gaba da karatu a Jami’ar ABU

Jami’ar Ahmadu Bello

Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) ta sanya Litinin 24 ga watan Oktoba da muke ciki a matsayin ranar da dalibanta za su dawo domin ci gaba da karatu.

Jami’ar ta fito da sanarwar ce a ranar Laraba, bayan janye yajin aikin kungiyar malamain jami’o’i (ASUU) da sukayi na tsawon wata takwas.

Daraktan Hulda da Jama’a na ABU, Auwalu Umar, a cikin wata sanarwa, ranar Laraba, ya ce Majalisar Jami’ar ce ta sanar da haka bayan zaman gaggawa da ta yi bayan janye yajin aikin kungiyar ASUU.

Majalisar Jami’ar, a zamanta na 516, ta amince da ranar dawowar da kuma sabunta jadawalin karatu na shekarar 2021/2022.

Ya ce, sabunta jadawalin karatun ya zama wajibi kasancewar wanda aka tsara a baya 25 bai yi aiki ba saboda yajin aikin ASUU.

An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

Klopp zai maye gurbin Nagelsmann a matsayin kocin Jamus

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya