Ranar Litinin za a sallame ni daga asibiti – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce anjima ranar Litinin za a sallame shi daga asibitin da yake jinya, kwanaki hudu bayan an kwantar da shi bayan kamuwarsa da cutar coronavirus. Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zai bar asibitin da misalin karfe 10:30 a agogon GMT yana mai cewa ya kara murmurewa. Trump […]

Ranar Litinin za a sallame ni daga asibiti – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce anjima ranar Litinin za a sallame shi daga asibitin da yake jinya, kwanaki hudu bayan an kwantar da shi bayan kamuwarsa da cutar coronavirus.

Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zai bar asibitin da misalin karfe 10:30 a agogon GMT yana mai cewa ya kara murmurewa.

Ya ce, “Ina kara samun sauki.

“Ku daina jin tsoron cutar COVID-19 ko ta hana ku sukuni. A karkashin mulki na, mun kirkiro wasu muhimman magunguna da za mu yi amfani da su.

“A zahirin gaskiya ma yanzu na fi lafiya fiye da shekaru 20 da suka gabata,” inji Trump.

Ya zuwa yanzu dai, akwai sama da mutum miliyan bakwai da dubu dari hudu da aka tabbatar sun kamu da cutar a Amurka, sama da 210,000 kuma su ka mutu kamar yadda alkaluman Jami’ar Johns Hopkins suka tabbatar.

Sallamar shugaban dai na zuwa a daidai lokacin da aka sami karin mutanen da suka kamu da cutar a fadar White House.

Akalla ma’aikata 12 dake da kusanci da shugaban ne aka tabbatar sun kamu da cutar, kuma yawancinsu sun halacci wani taro da aka yi ranar 26 ga watan Satumban da ya gabata, wanda ake kyautata zaton shine ummul aba’isun yaduwarta.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma’a ne shugaba Trump ya tabbatar da cewa shi da uwar gidansa, Misis Melania Trump sun kamu da cutar, kafin kuma daga bisani a garzaya da shi asibiti kashe-gari.

Rashin lafiyar kuma ta zo ne lokacin da ake tsaka da yakin neman zaben shugaban kasar da zai gudana a watan Nuwamba mai zuwa, inda zai fafata da dan takarar jam’iyyar Democrat, Joe Biden.