Ranar ma’aikata ta bana da batun sabon albashi mafi kankanta
A ranar Laraba 1 ga wannan watan na Mayu miliyoyin ma`aikatan kasar nan suka bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen bikon ranar Ma`aikata ta duniya. Tarihin bikin ranar ya dauko asali ne daga Amurka, inda wasu gungun ma`aikata na birnin New York a ranar 5 ga watan Satumban 1882, suka fara bikin ranar da […]
A ranar Laraba 1 ga wannan watan na Mayu miliyoyin ma`aikatan kasar nan suka bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen bikon ranar Ma`aikata ta duniya.
Tarihin bikin ranar ya dauko asali ne daga Amurka, inda wasu gungun ma`aikata na birnin New York a ranar 5 ga watan Satumban 1882, suka fara bikin ranar da sunan Ranar Kwadago ta duniya. Daga bisani kuma a ranar 1 ga watan Mayun 1886, ranar ta fara zama ranar hutu a dai kasar ta Amurka inda wasu ma`aikata sama da 300,000, daga fannonin kwadago daban-daban 13,000, a dai kasar ta Amurka suka bar wuraren ayyukansu don bikin ranar a Ranar Ma`aikatan ta farko a duniya.
Mu a nan kasar, gwamnatin farar hula ta farko a inuwar jam`iyyar PRP a Jihar Kano marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, ita ta fara mayar da ranar 1 ga watan Mayun 1981, ta zama ranar hutu a kasar nan. Da shekarar ta zagayo, wato 1982, sai gwamnatin farar hula ta jam`iyyar NPN, a karkashin jagorancin marigayi shugaban kasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ta mayar da ranar a zaman ranar hutu a kasa baki daya.
Ma`aikata, a kasashen duniya daban-daban, musamman shugabannin kwadago, bayan hutu da ranar take kasancewa, sukan yi amfani da ranar wajen shirya kayataccen biki da ke kunshe da jerin gwanon kungiyoyin ma`aikata daban-daban a kasa da jihohi. Bayan jerin gwanon shugabannin kungiyoyin ma`aikatan da ma masu mulki, irin su shugaban kasa (a tarayya) da gwamnoni (a jihohi), wajen gabatar da jawabai iri-iri. Shugabannin kungiyoyin kwadagon kan gabatar da koke-kokensu a kan irin matsalolin da suke damun ma`aikata da yadda suke ganin ya kamata a shawo kansu. Su kuma shugabannin, sukan mayar da martani a kan irin wadancan koke-koke da yadda suka magancesu, ko suke da aniyar magancesu. Haka al`adar bikin Ranar ma`aikatan take a duk fadin duniya.
Babban abin da ya fi daukar hankali a bikin ranar ma`aikatan ta duniya ta bana, a dukkan fadin kasar nan, shi ne batun fara aiwatar da sabon karin albashi mafi kankanta na Naira dubu 30, sabon karin albashin da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kai a watan Afrilun da ya gabata, bayan shafe sama da shekara guda ana ta kai- komo tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnatoci.
A cikin jawabinsu na hadin guiwa, shugabannin kungiyoyin kwadagon kasar nan biyu, wato Kwamared Ayuba Wabba na NLC da Kwamared Bobboi Bala Kaigama na TUC, sun koka matuka a kan hauhawar farashin kayayyaki inda suka ninka har sau biyu da rashin ingantaccen albashi, a zaman manyan abubuwan da suke kara tauye rayuwar ma`aikatan kasar. Baya ga dawainiyar ciyar da iyali da tsadar kudaden haya.
Kazalika, shugabannin kungiyoyin kwadagon biyu, sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta fara aiwatar da biyan sabon karin albashi mafi kankanta na Naira dubu 30. Sun kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta rika watsi da shawarwarin da Asusun bada lamuni na duniya wato IMF, yake ba ta a kan batutuwan da suka shafi janye sassaucin farashin man fetur, wanda ke nufin a kara farashin man. Shugabannin kungiyoyin kwadogon NLC da TUC sun kara da cewa kullum shigowar IMF a kan harkokin tattalin arzikin kasar nan ba sa wuce a kan batuwa uku. Wato a janye tallafin farashin man fetur, a karya darajar Naira, sannan a bude kan iyakokin kasar nan, ta yadda kowane tarkace zai iya shigowa, dukkan wadannan abubuwa, ba abin da suke yi illa kara jefa rayuwar talakan kasar cikin mawuyacin hali.
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo shi ya wakilci shugaba Buhari a wajen bikin da aka yi a Abuja, kasancewar a lokacin shugaban kasar na birnin Landan, amma dai shugaba Buhari ya aiko da sakon cewa gwamnatinsa za ta biya sabon karin albashin na mafi karanci wato Naira dubu 30, kamar yadda ya fadi a lokacin da yake sa hannu a kan Dokar da ta tabbatar da sabon karin albashin.
A jihohi da aka yi bikin ranar Ma`aikatan ta Duniya, wasu gwamnoni sun tabbatar wa ma`akatansu cewa za su biya sabon tsarin albashin, ba tare da ko sisin kwabo ya yi ciwon kai ba. Yayin da a wasu jihohin, gwamnonin sun furta cewa ba za su iya biyan sabon tsarin albashin ba. Wasu gwamnonin jihohin kuwa gum suka yi da bakunansu, duk kuwa da shugabannin kungiyoyin kwadago na jihohin sun ta da batun lallai sai gwamnonin su hamzarta fara aiki da sabon tsarin albashin.
Daga cikin gwamnonin jihohin da suka ce da ma`aikatansu, su sha kuruminsu a kan za su biya sabon tsarin albashin, ba tare da sisin kwabo ya yi ciwon kai ba, akwai Gwamnan Jihar Zamfara kuma shugaban Kungiyar gwamnonin jihohin kasar nan Alhaji Abdulaziz Yari da na Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da na Jihar Edo Mista Godwin Obaseki da na Bayelsa Mista Seriaka Dickson. Shi ma gwamnan Jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi, tabbaci ya ba ma`aikatan jihar cewa zai biya su yadda doka ta tanada.
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari a sakon da shugaban ma`aikatan jihar Alhaji Idris Tune ya karanta a madadinsa cewa ya yi ba zai ba ma`aikatan jihar tabbacin zai iya biyan sabon tsarin albashin ba, har sai sun tattauna da shugabannin kungiyoyin kwadago na jihar tukuna. A Jihar Kogi kuwa, jihar da gwamnanta Alhaji Yahaya Bello, gwamnan da ya fi kowane gwamna taurin bashin biyan hakkokin ma`aikata, abin da ya kai a jihar ba albashi, ba fansho, bare giratuti, gwamnan da zai sake neman komawa mulkin jihar a karo na biyu a zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 2-11-19. Shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Mista Onu Edoko ya kalubalanci gwamnan da cewa muddin bai biya su albashin watanni bakwai da suke bi ba, to, a wannan ranar ma`aikatan za su yanke masa hukuncin yankan kauna, muddin dai Hukumar zabe ta INEC, za ta kirga kuri`unsu kamar yadda suka kada su. Amma dai shi shugaban ma`aikatan jihar da ya wakilci gwamnan cewa ya albashin watanni biyar ma`aikatan ke bi, kuma gwamnati za ta zauna da su a kan yadda za a aiwatar da sabon tsarin albashin.
A jihohin Sakkwato da Legas da Taraba da Osun, duk da gwamnoninsu sun tura wakilansu wajen bikin ranar ma`aikatan ta duniya, amma gwamnonin sun ki cewa uffan a kan makomar biya ko kin biyan sabon tsarin albashin, sai dai wakilan sun buge da ba ma`aikatan jihohin labarin irin kyautatawar da suka yi masu a cikin mulkinsu.
Ba ko shakka ranar ma`aikatan ta duniya ta bana ta yi armashi, musamman ga shugabannin kungiyoyin kwadago da suka yi mata kallon ta zo a daidai lokacin da aka kawo karshen gwagwarmayar neman karin albashin da suka dade suna yi shekara da shekaru. Saura da me? Muna fata a badi in Allah Ya kai mu `yan kwadagon su zo da labarin kowace jiha tana biyan sabon tsarin albashin a kan kari. Karin albashin da ba makawa zai kara kawo tsadar rayuwa ga `yan kasa, kasancewar tarihi ya nuna ba a taba yin karin albashi a kasar nan, alhali farashin kayayyaki ba su yi tashin gwauron zabo ba.