Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya: Tambaya Da Amsa
daya daga cikin ’yan kwamitin watsa labarai da ke shirye-shiryen gudanar da gagarumin bikin Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya, ya yi bayani dalla-dalla dangane da bikin, kamar haka: Tambaya: Me ake nufi da Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya? Amsa: Rana ce da marubutan Hausa ke burin haduwa da juna, tsakanin manyan marubuta da kanana, shahararru […]
daya daga cikin ’yan kwamitin watsa labarai da ke shirye-shiryen gudanar da gagarumin bikin Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya, ya yi bayani dalla-dalla dangane da bikin, kamar haka:
Tambaya: Me ake nufi da Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya?
Amsa: Rana ce da marubutan Hausa ke burin haduwa da juna, tsakanin manyan marubuta da kanana, shahararru da masu tasowa domin gudanar da taron kara wa juna sani, musayar ra’ayi da sauraron jawabai daga masana da ke fadin duniya cikin harshen Hausa. Ana sa ran wannan taron ya zama an gudanar da shi a kebantattun lokuta domin zaburar da marubutan Hausa su ci gaba da bunkasa harshen, yadda amonsa zai ci gaba wanzuwa a fadin duniya.
Tambaya: Bayan wadannan abubuwan da aka lissafa, shin za a gudanar da wasu da ba a fada ba a sama ba?
Amsa: Na’am, ana sa ran za a yi baje kolin sabbi da tsoffin littattafai, za a gabatar da kasidu da rubutattun wakoki da gajerun labaru sannan za a gabatar da gasar gajerun labaru idan hali ya yi. Bayan haka kuma, makaranta da manazarta za su samu zarafin ganawa da marubuta tare da sadar da zumunci tsakanin kafafen watsa labarai da marubuta, manazarta, mawaka da makaranta. Haka kuma akwai ziyara ta musamman da ake sa rai marubutan za su kai wa fitattun jama’a a wannan lokaci.
Tambaya: Yaushe za a yi wannan taron?
Amsa: Za a gudanar da wannan taron karshen watan Oktoba.
Tambaya: Kwanaki nawa za a gudanar da taron?
Amsa: Kwana biyu.
Tambaya: Wa da wa ake gayyata?
Amsa: Ana gayyatar kowa da kowa da suka hada da marubutan jiya da na yau, manazarta, malamai, alkalai, ma’aikatan gwamnti, ’yan jarida, makaranta da sauran jama’ar gari.
Tambaya: Wane alfanu ko tasiri wannan taro zai yi ga marubuta, manazarta da makaranta?
Amsa: Kamar yadda bayani ya nuna, akwai kara wa juna sani tare kasidu da mukaloli da za a gabatar, wannan kadai zai kaifafa basirar marubuci ya nakalci wasu dabarun kulla zaren labari ba tare da wahala ba. Manazarci kuwa zai samu zarafin ganawa da marubuci tare da warware wata sarkakiya da ke tsakaninsu yayin nazari. Makaranci zai samu ganawa da marubuci tare da samun wasu amsoshin tambayoyin da yake bukata. Uwa uba kuma taron zai zama sila ta sadar da zumunci tsakanin wadannan rukunai da ma wasunsu.
Tambaya: Shin an taba gudanar da irin wannan taron a baya?
Amsa: Kodayake an sha gudanar da tarukan da suka shafi adabi da harshen Hausa, to amma dai ba a yi wani a baya da aka kira shi da wannan suna ba, watau Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya. Muna fata wannan ya zama tushen samar da tabbataccen hadin kai da kuma dorewar darajar rubuce-rubucen Hausa.