Kungiyar matan ‘yan sanda ta raba wa mata 100 kayan abinci a Gombe
Kungiyar ta raba wa mata sama da 100 kayan abinci a jihar.
Kungiyar Matan Jami’an ‘Yan Sanda (POWA) a Jihar Gombe, ta tallafa wa mata sama da 100 da kayan abinci.
Rabon tallafin ya samu jagorancin uwar gidan Babban Sufeon ‘Yan Sandan Najeriya, Misis Elizabeth Egbetokun, inda mata marasa galihu suka ci moriya da kuma matan ‘yan sanda da mazajen su suka mutu da wadanda suka jikkata.
- An tsinci gawar wani mutum a kan titi a Kano
- Ɗalibai a jihohi 14 na cikin haɗarin ’yan bindiga — Gwamnatin Tarayya
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce taron na bana mai taken ‘Zuba Jari kan kula da harkokin mata’ ya gudana ne a hedikwatar ‘yan sandan ta jihar.
Shugabar kungiyar a Jihar Gombe, uwar gidan Kwamishinan ‘yan sandan jihar Misis Hayatu, ta jaddada muhimmancin karfafa wa mata da inganta daidaiton jinsi.
Ta ce yana da kyau masu hali suke taimakon marasa karfi domin an shiga wata irin rayuwa ta kunci.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Gombe, Hayatu Usman, shi ne ya gabatar da rabon kayan abincin da kungiyar ta yi na bana a jihar.
Kwamishinan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, DCP Bashir Mustapha, ya ce kungiyar POWA reshen jihar, ta jaddada kudirinta na tallafa wa mata da kuma kwato musu hakkokinsu saboda irin rawar da suke takawa wajen ci gaban al’umma.
Wasu daga cikin matan da suka amfana da tallafin sun yaba wa kungiyar POWA kan yadda ta tallafa musu a lokacin da suke da bukatar taimako.