Ranar Mata ta Duniya: Emefiele ya yi alkawarin cike gibin jinsi a CBN

Ranar 19 ga watan Maris, 2019, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya taya matan bankin murna a matsayin daya daga cikin shagalin Ranar Mata ta Duniya. Shagalin wanda daukacin mata ma’aikata na bankin suka halarta da bakin da aka gayyata, ya samu halartar Ministar Kudi, Malama Zainab Shamsuna Ahmed da sauran manyan baki. Gwamnan Bankin CBN, […]

Ranar Mata ta Duniya: Emefiele ya yi alkawarin cike gibin jinsi a CBN

Ranar Mata ta Duniya: Emefiele ya yi alkawarin cike gibin jinsi a CBN

Ranar 19 ga watan Maris, 2019, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya taya matan bankin murna a matsayin daya daga cikin shagalin Ranar Mata ta Duniya. Shagalin wanda daukacin mata ma’aikata na bankin suka halarta da bakin da aka gayyata, ya samu halartar Ministar Kudi, Malama Zainab Shamsuna Ahmed da sauran manyan baki.

Gwamnan Bankin CBN, Godwin I. Emefiele ya ce duk da hujjar da ake da ita da ta nuna cewa daidaiton jinsi yana daya daga cikin ci gaban tattalin arziki kuma muhimmin matakin cimma kudirin bunkasa kasa na shekarar 2030, ci gaban da ake da shi dangane da daidaiton jinsi yana tafiyar hawainiya.

Da yake jawabi a wurin taron Ranar Mata ta Duniya na bana da aka yi a hedikwatar bankin da ke Abuja, Emefiele ya ce “Kamar yadda kuka sani Ranar Mata ta Duniya ta bayar da dama ba wai kawai a yi waiwaye kan ci gaban da aka samu ba ne har da wayar da kan jama’a tare da jaddada kudirin da ake da shi na tabbatar da daidaton jinsi da kuma karfafa mata.”

Ya ce taken Ranar Mata ta Duniya ta bana ya mayar da hankali ne kan kirkiro hanyoyin tabbatar da daidaiton jinsi da tallafa wa mata. Ya bayyana cewa bankin CBN tuni ya riga ya mayar da hankali kan tabbatar da daidaito a tsakanin jinsi. Ya ce “Taken ranar ya dace kuma ya zo daidai da lokaci don yana ba mu damar karfafa matakinmu na tallafa wa mata wanda muka yi imanin shi ne abu mafi muhimmanci dangane da tattalin arziki da walwala.”

Ya ce “Bari in dan yi tsokaci kan binciken da masana suka yi da ke nuna muhimancin daidaiton jinsi a bunkasar tattalin arziki:

Wani kwararre mai suna McKinsey da ya yi bincike a shekarar 2017 ya bayyana cewa idan da gudunmawar da mata ke bai wa tattalin arziki ta zo daidai da ta maza to da babu shakka za a samu karin Dala tiriliyan 28 ga ci gaban tattalin arziki duniya a shekarar 2025.

Wani rahoto da aka fitar a taron duniya kan tattalin arziki da gibin daidaiton jinsi a shekarar 2018 ya nuna cewa akwai kimanin kashi 32 cikin 100 na gibin daidaiton jinsi da ke bukatar a magance kuma hakan na nuna daukacin gibin da ake da shi a tsakanin jinsi za a magance shi nan da shekara 108.

Wani bincike da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar ya nuna cewa damawa da mata a cikin al’amura a matsayin  masu samarwa da kuma sanya ido kan hada-hadar kudi yana da amfani fiye da magance rashin daidaiton jinsi. Magance gibin daidaiton jinsi zai samar da daidaito a tsarin banki tare da bunkasa ci gaban tattalin arziki. Zai iya bayar da gudunmawa dangane da karfafa tsarin kudi da kuma dokokin kasafin kudi.

Binciken ya gano rashin daidaiton jinsi a fannin shugabanci yana nuna bambanci a tsarin banki. Bankunan da suke da mata da yawa a hukumomin gudanarwarsu sun fi samun jari mai karfi da karancin biyan bashi tare da jure wa duk wani kalubale da aka iya tasowa.

Wani masani mai suna Lagarde da ya yi bincike a shekarar 2019 ya kara da cewa kasancewar mata da yawa a mukamai tare da barinsu a kan mukaman yana da alaka da bunkasar kadara. Idan bankuna suka kara yawan mata a manyan mukamai bankunan za su samu daidaito.

“Yayin da muke murna a yau bari in tunatar da mu cewa kodayake daidaiton jinsi ya bunkasa a Bankin CBN a ’yan shekarun nan, amma ya zama wajibi a kara kokari don cimma daidaiton jinsi. Muna murnar ci gaba a yau saboda ci gaban da aka samu wajen magance rashin daidaiton jinsi a Bankin CBN. Matakan da bankin ya dauka na bunkasa daidaito a wurin aiki sun hada da bayar da horo da bunkasa dabaru da karin ma’aikata da karin gurabe ga mata da kuma damawa da mata da tallafa wa mata ma’aikata don samar da daidaiton aiki da kula da iyali ta hanyar kula da yara da karin hutun haihuwa da sauransu, da ba su horo da karin ilimi don cimma burin ma’aikatarmu. Wannan kokari ya kai ga ci gaba wajen rage gibin da ake da shi na daidaiton jinsi a bankin. Abin farin cikin ne yau a ce mata suna da kashi 29 a yawan ma’aikatan bankin da daraktoci kashi 29 da daraktocin sassa takwas da Darakta Janar daya fiye da kashi 26 cikin 100 na ma’aikatan bankin da kuma kashi 25 na daraktocin bankin a shekarar 2014. Haka kuma uku daga cikin mambobin hukumar gudanarwar bankin mata ne wanda hakan ke nuna kashi 27 cikin 100,” inji shi.

Ya bayyana cewa “Za ku yarda da ni cewa  mata suna bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki ko dai a matsayinsu na ’yan kasuwa ko masu kamfanoni ko manoma ko masu daukar ma’aikata a wata sana’a. Duk da haka mata masu sana’o’i suna fuskantar matsaloli wajen tafiyar da sana’o’insu da mallaka da kuma bunkasa kasuwancin.”

Sakamakon wadannan kalubale ne bankin ya bullo da tallafin jinsi wanda ya mayar da hankali kan saka jari ga mata ta yadda za su samu tallafi daga hada-hadar kudi masu yawa kamar asusun kanana da matsakaitan sana’o’i wanda a kashi 60 cikin 100 aka ware wa matan da ke hada-hadar kasuwanci da shirin samun bashi da shirin bayar da bashi ga manoma da sauransu.

Manyan baki maza da mata ina son in nanata kokarin bankin wajen gini kan nasarorin da aka samu don bunkasa tattalin arzikin mata da daidaiton jinsi. A karshe ina  tunatar da mu da wani furuci da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi a shekarar 2018 inda ya ce “Cimma daidaiton jinsi da tallafa wa mata da ’yan mata wani batu ne mai sarkakiya kuma babban kalubale ne ga ’yancin dan Adam a duniyarmu. Hakika wannan kira ne  don a yi aiki yayin da muke murnar nasarori da kuma gudunmawar matan bankin CBN ina son in jaddada kokarinmu don kammala wannan batu,” inji shi.

Emefiele ya yaba wa baki a taron musamman ma Ministar Kudi, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed don bayar da lokacinta ta halarci taron duk da dimbin ayyukan da ke gabanta.