Ranar Mata Ta Duniya: ‘Haƙiƙanin Abin Da Mata Suke Buƙata’
Ranar 8 ga watan Maris Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar mata ta duniya.
Irin wannan rana ta 8 ga watan Maris Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Mata ta Duniya domin duba rawar da suke takawa a fannoni daban-daban.
Wasu na ganin mata da dama da ke yi wa junansu hassada ya sa ba a samun cigaban da ya kamata, yayin da ake ganin ya kamata a rika tallafa wa cigaban mata da kuma habaka tunaninsu.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Wutar Lantarki Ke Durkusar Da Sana’o’i
- ‘Amfani Da Tsoffin Takardun Naira Zai Iya Jefa Mutum A Matsala’
Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akwai mata kusan miliyan 342 da ke fuskantar barazanar fadawa kangin talauci nan da shekarar 2030.
Shin ta ya za a kauce wa hakan?
Shirin Najeriya a Yau ya yi duba kan wannan rana da kuma yadda za a tallafi matan a fannoni daba-daban.
Domin sauke shirin, latsa nan