Ranar Maulidi

Ranar Talatar da ta gabata ce Musulmi suka gudanar da bikin ranar maulidi, wato ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW). Ana bikin maulidi ne a duk ranar 12 ga watan 3 wato Rabi’ul Awwal na shekarar Musulunci, wannan ne ya sa ranar take da bambanci a kalandar Turawa. Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutun […]

Ranar Maulidi
Ranar Maulidi

Ranar Talatar da ta gabata ce Musulmi suka gudanar da bikin ranar maulidi, wato ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW). Ana bikin maulidi ne a duk ranar 12 ga watan 3 wato Rabi’ul Awwal na shekarar Musulunci, wannan ne ya sa ranar take da bambanci a kalandar Turawa.

Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutun ranar Talata da ta gabata domin murnar ranar ta maulidin bana, wato shekara 1440 bayan hijira.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya, a lokacin da yake jawabi game da ranar, ya bukaci Musulmi da su yi koyi da karantarwar Annabi, wanda ya ta’allaka da tausayi da sadaka da kaunar juna da kuma zaman lafiya da sauransu. Sannan kuma ya bukaci duk mutanen Najeriya da su yi koyi da wadannan dabi’u domin magance matsalolin da suka dabaibaye kasar. Dambazau ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya a shirye take ta tabbatar da kasancewar kasar dunkulalla, don haka ne za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa an gudanar da zabukan badi cikin nasara kuma ba gara ba zago.

A daidai lokacin da wasu Musulmi suke bikin maulidi a duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal, su kuma malaman Shi’a suna ganin ranar 17 ga wata ce. Tarihin wannan biki yana komawa ne tun farkon Musulunci, sannan kuma a zamanin mulkin Usmaniyya ne aka ayyana ranar a matsayin ranar biki a shekarar 1588. Amma wasu bangare na Musulmi da suka hada da Wahabiyawa da Salafiyya da Ahmadiyya ba su amince da bikin ba, inda suke kallon ranar a matsayin kirkira da bai da amfani wato bidi’a.

Sakon Manzon Allah a kullum shi ne zaman lafiya da riko da gaskiya da amana da kuma watsi da duk wani lamari koma bayan wadannan. Ranar maulidi na ba Musulmi damar tunawa da ayyukan kwarai na Manzon Allah da kuma sakon da ya kawo daga Allah. Don haka ne ranar ta zama ta musamman ga ’yan Najeriya domin su fahimci ma’anar addini da kuma koyi da koyarwarsa. Ba shakka addini na da matukar muhimmanci wajen juya akalar mutum, sannan kuma damar bauta da kuma koyi da addinin da mutum ya zaba yana nan a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan.

A daidai lokacin da zabukan 2019 ke kusantowa, Najeriya na fama da matsalolin da suka hada da karancin ababen more rayuwa da karuwar matsalar bambamcin siyasa da matsalar rikicin kabilanci da tabarbarewar ilimi. Don haka ne muke kira ga ’yan Najeriya da su rika amfani da irin wannan rana domin tuna yanayin da kasar ke ciki da kuma tunani a kan muhimmancin hakuri da sadaukarwa da ladabi da kuma son juna. Lallai wadannan abubuwan koyi masu kyau babu lokacin da ake bukatarsu fiye da yanzu.

Ya kamata ’yan Najeriya su rika mutunta addinan juna, da kuma amfani da hanyar tattaunawa maimakon yadda abin ke neman zama ruwan dare yanzu na amfani da rikici da hayaniya da batanci da sauransu idan an samu bambamci. Ta hanyar amfani da hakan ne kawai ’yan Najeriya za su magance matsalar kin juna da rikicin addini da ta’addanci da yunwa da cututtuka da kuma koma baya da ake samu, wanda kuma yana cikin abin da maulidi ke koyarwa.

Ranar Maulidi na koyar da son juna da hakuri da sadaukarwa ta hanyar adana tarihinmu, da kuma uwa-uba kauna da aiki wajen samar da kasa da dukkanmu za mu yi alfahari da ita. Duba da irin muhimmancin da addini ke da shi ga al’umma, ya kamata addinai su zama masu koyar da bukatar samun ci gaba. Don haka duk wani dan Najeriya nagari da ke kaunar kasar nan, ya kamata ya yi amfani da ranar maulidi domin nuna albarkar da Allah Ya yi wa kasar na dimbim mutane daban-dabam masu addinai da kabilu mabambanta.

Ita kuma gwamnati a bangarenta, ya kamata ta yi amfani da ayyuka da kudurori masu kyau wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta. Da fata an yi bikin ranar maulidi lafiya.