Ranar Polio: Sai da rigakafi za a iya dakile cutar shan-inna a duniya —WHO

Hukumar ta ce shan inna na daga cikin cututtukan da ke yi wa al’umma barazana a duniya, musamman ma kananan yara.

Ranar Polio: Sai da rigakafi za a iya dakile cutar shan-inna a duniya —WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sai an bai wa shirin yi wa kananan yara riga-kafin shan inna muhimmancin gaske kafin a iya dakile cutar a fadin duniya.

Ta ce sanya ido da kuma bin diddigin yadda ake aiwatar da ba da riga-kafin cutar ga yara, na daga cikin matakai masu muhimmancin wajen yaki da wannan cuta.

WHO ta yi wannan bayani ne a shafinta na intanet, albarkacin zagayowar Ranar Yaki da Cutar Shan Inna ta Duniya ta 2022.

Hukumar ta ce shan inna na daga cikin cututtukan da ke yi wa al’umma barazana a duniya, musamman ma kananan yara.

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce, Najeriya ta yi nasarar a yaki da cutar shan inna, domin kuwa rabon da a samu mai dauke da cutar a kasar tun a 2016.

Ranar 24 ga Oktoba na kowace shekara, ita ce ranar Majalisar Dinkin Duniya ta ware don karfafa yaki da cutar ta shan inna.