Ranar Sallah: El-Rufa’i zai yi sintiri a iyakar Kano da Kaduna
Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya shaida cewa da kansa zai yi sunturi akan iyakar jihar Kaduna da Kano a ranar sallah karama domin tabbatar da cewa, ba wani mutum da zai ketaro daga Kano ya shiga Kaduna. Hakan na nufin wani kokarin da yake yi ne kare yaduwar annobar COVID-19 a jihar. Tuni gwamnan […]
Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya shaida cewa da kansa zai yi sunturi akan iyakar jihar Kaduna da Kano a ranar sallah karama domin tabbatar da cewa, ba wani mutum da zai ketaro daga Kano ya shiga Kaduna.
Hakan na nufin wani kokarin da yake yi ne kare yaduwar annobar COVID-19 a jihar.
Tuni gwamnan ya sauya ranakun da yake bai wa mazauna jihar damar fita domin su sayi kayayyakin masarufi, daga ranar Laraba da Asabar zuwa ranar Laraba da Alhamis, inda ya kaucewa ranar Asabar ranar da ake zaton zata kasance ranar Sallah bayan kammala ibadar azumin watan Ramadan.
- Dokar kulle: El-Rufa’i ya nemi afuwar jama’a
- Sallar Idi: El-Rufa’i yayi watsi da bukatar limaman Kaduna
- ‘Da biyu a ka yi sauyin ranakun doka a Kaduna’
Malam Nasiru El-Rufa’i ya bada sanarwar sintirin da zai yi ne da irin salo na gargadi a locacin da yake zantawa ta wasu gidajen rediyo a Kaduna.
“Zan tabbatar na shiga tawagar ‘yan sintirin da za suyi aiki akan iyakokin Kano da kaduna a ranar sallah, zan kasance a wajen tun da sanyin safiya har dare domin na tabbatar babu wani da zai sulalo ya shigo Kaduna.
Gwamnan ya nuna takaicinsa duba da yadda ake samun cunkoson ababan hawa daga ciki da wajen jihar Kaduna, duk da matakin gwamnatin tarayya na hana zirga-zirgar jama’a a tsakanin jihohin kasar nan.
Ya ce, laifin jami’an tsaro ne da ke karbar cin hanci ko na goro a wajen matafiya, wadanda suke kawo nakasu ga kokarin gwamnati na kare yaduwar annobar coronavirus.
“Akasarin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar mutane ne da suke tafiye-tafiye, mun yi namu kokarin amma wasu jami’an tsaro na yi mana bita da kulle, muna sane da cewa sau tari direbobin motocin haya na biyan su kudi, su kyalesu su shigo Kaduna” in ji shi.
Tuni dai gwamnatin jihar Kano da ke makwabtaka da Kaduna ta bada sanarwar bai wa mazauna jihar damar walwala a ranaku uku ciki harda ranar Asabar da ake sa ran tashi da sallar Idi da kuma jajiberin ta.