Ranar Sallah: Kasashen Afirka da suka yi Idi kafin Saudiyya
Al’umar Musulmi a wasu yankuna na gabashin Afirka da yammacin ta sun gundunar da hawan Idin sallah karama a ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, duk da cewa mafi yawa daga cikin Musulmin ana sa ran za su yi sallar ne a ranar Lahadi. A kasar Somaliya Ministan al’amuran Addinai na kasar Sheikh Nur Mohamed Hassan, ya […]
Al’umar Musulmi a wasu yankuna na gabashin Afirka da yammacin ta sun gundunar da hawan Idin sallah karama a ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, duk da cewa mafi yawa daga cikin Musulmin ana sa ran za su yi sallar ne a ranar Lahadi.
A kasar Somaliya Ministan al’amuran Addinai na kasar Sheikh Nur Mohamed Hassan, ya bada sanarwar ranar Asabar a matsayin ranar Sallar Idi karama a kasar, sanarwar tazo ne a tsakar daren Juma’a bayan da aka sami wasu mutum takwas da suka shaida ganin watan a yankin Birnin Mogadishu.
Haka zalika yawancin kasashen Afirka ta Yamma an yi hawan Idin sallah karama a ranar Asabar a hukumance, kasashen da suka hadar da Niger zuwa Senegal, da Mali, da Gambia, da Senegal da kuma Burkina Faso, da Ivory Coast wadannan sune kasashen da suka yi hawan Idin sallah karama gabanin kasar Saudiyya.
Ranar Idin A Najeriya
A Najeriya Mai alfarma Sarkin Musulmin Kasar Alhaji Sa’ad Abubakar, shi ke da alhakin sanar da ganin watan azumin Ramandan da na Shawwal.
Sarkin Musulmin ya ayyana ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu a matsayin ranar Idin sallah karama, bisa dalilai na rashin ganin wata a kasar, lamarin da jama’a da dama suka yi ta suka a kasar, inda suke ganin matakin ya biyo bayan sanarwar da kasar Saudiyya tayi ne na yin sallar Idin a ranar Lahadi a kasa mai tsarki.
Wasu sun yi sallah ranar Asabar
A bana dai a Najeriya an sami rashin jituwa a sha’anin ganin watan sallar Idin, ta yadda shahararren malamin nan na kasar Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya bai wa mabiyansa umarnin ajje azumin ramadan tare da yin sallar idin a ranar Asabar.
Shaikh Dahiru usman Bauchi ya jagoranci sallar Idin a ranar Asabar a harabar gidansa da ke Bauchi, haka zalika a jihohin Yobe da Sakkwato ma an yi hawan sallar Idin a ranar Asabar.
Ranar juma’a ‘yan Shi’a suka yi sallah
A daya bangaren a Najeriya mabiya Shi’a sun gudanar da hawan sallar Idin tun a ranar Juma’a a garuruwan Sakwatto da Zariya bayan da suka ce sun ga watan tun da yammacin Alhamis.
Ana cigaba da tafaka muhawara akan ganin watan
Zuwa yanzu dai batun da yafi daukar hankalin al’umar Najeriya shine na ganin wata, inda ake cigaba da tafaka muhawara musamman a kafafan sada zumunta sai dai malamai da dama na kokarin fahimtar da jama’a akan sun rungumin duk abin da suke ganin sun fi nutsuwa da shi a zuciyar su.
Sallar Idi a lokacin Annoba
A bana Idin sallah karama yazo ne a lokacin da annobar coronavirus ke addabar duniya,matakin kare yaduwar annobar ya sanya a Najeriya za a yi sallar Idin ne a gida a jihohi da dama da suka hadar da mafi akasarin jihohin kudancin kasar da suka hadar da cibiyar hada-hadar kasar wato jihar Legas wacce ita ce kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar COVID-19.
A Arewacin kasar an sami wasu gwamnoni da suka saukaka dokar kulle domin baiwa al’ummar su daman yin sallar Idin bisa daukar matakan kariyar annobar, jihohin da suka bada damar sun hadar da jihar Kano, da Borno da jihar Bauchi.
Anobbar coronavirus ta sauya fasalin sallar idin na bana inda za ayi batare da gudanar da bukukuwan al’adu da aka saba gabatarwa ba, wadanda suka hadar da hawan daba, yawan sallah da kuma shagulgulan bukukuwa da aka saba gabatarwa a lokacin sallar a Kudu maso Yammacin kasar
Bugu da kari annabar da matakan kariyarta na zaman kulle sun taba tattalin arzikin jama’a da dama tayadda sallar bana tazo masu a wani yanayi mai wuya lamarin da ya sanya jama’a da dama basu sami damar yiwa ‘yan’ayan su dinkin sallah ba, yayin da jama’a da dama ke neman abin da za su saka a bakin su, wadanda suka ce a bana ba ta kayan sallah suke ba, lamarin da ya sanya teloli da yan kasuwa kokawa duba da yadda sallar banar ta riske su a wani yanayi na rashin kasuwa.