Ranar Sallah: Mutane 2 sun rasu 3 sun tsallake rijiya da baya

Mutane uku sun tsallake rijiya da baya a hatsarin motar

Ranar Sallah: Mutane 2 sun rasu 3 sun tsallake rijiya da baya

Wani hatsarin mota (tsohuwar ajiya)

An tabbatar da rasuwar mutane biyu a ranar Sallar Layya a sakamakon taho-mu-gama da wasu motoci suka yi a kan babbar hanyar Sagamu zuwa Ijebu-Ode da ke Jihar Ogun.

Kakakin Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Ogun, Florence Okpe, ta sanar cewa wasu mutane uku sun samu rauni sakamakon hatsarin, wanda ya ritsa da babbar mota kirar Howo da wata karama kirar Toyota Camry.

Florence Okpe, ta dora laifin aukuwar hatsarin da misalin kare 12 na rana a kan gudun wuce misali, da ya sa daya daga cikin motocin ta kwace tare da yin karo da dayar.

Okpe ta ce, “Mutane biyar, namiji daya da mata hudu ne abin ya ritsa da su, kuma a cikinsu namijin da mace daya sun rasu, ragowar matan kuma sun samu raunuka.”

Jami’ar ta bayyana cewa an kai dukkansu Babban Asibitin da ke Ijebu Ode.

Kwamandan Hukumar na jihar, Anthony Uga, yayin mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar ya ja hankalin masu amfani da ababen hawa da su rika kiyaye dokokin tuki.

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa

Gwamnati ta ba da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suke Haddasa Turmutsutsu A Najeriya