Ranar samun ’yancin kai: Gwamnatin Najeriya ta ayyana Litinin a matsayin hutu
Ranar Lahadi mai zuwa ce dai Najeriya za ta cika shekara 63 da samun ’yancin kai
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba a matsayin hutu albarkacin cikar Najeriya shekara 63 da samun ’yancin kai.
Ministan Al’amuran Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, a madadin gwamnatin.
- Zaben Kaduna: Kotu ta yi watsi da shaidun PDP
- Kotu ta fara karanta hukuncinta kan zaben Zaben Gwamnan Kaduna
Ministan ya kuma taya dukkan ’yan kasar na gida da na ketare murnar zagayowar.
Sanarwar, wacce Babban Sakataren ma’aikatar, Oluwatoyin Akinlade, ta ba ’yan Najeriya tabbacin gwamnati na ci gaba da magance matsalolin da suka addabi kasar.
Ministan ya ce duk da cewa tarin kalubalen da suke fuskantar Najeriya ba iya kasar suke shafa ba, amma gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance su.